Le Républicain (Nijar)
Appearance
|
periodical (en) | |
| Bayanai | |
| Farawa | 1991 |
| Laƙabi | Le Républicain |
| Harshen aiki ko suna | Faransanci |
Jaridar Le Républicain dai, jarida ce ta mako-mako da ake wallafawa a Harshen Faransanci daga babban birnin Niamey na Nijar. Ana buga jaridar a duk ranar Alhamis, kuma ana gudanar da ita daga ofisoshi a Place du Petit Marché, Niamey. An kafa Le Républicain a shekara ta 1991, biyo bayan sassauta dokokin kafofin watsa labarai, jaridar mallakar Mama Abu, wata mai kula da kwamfuta kuma mai shirya harkokin sabgar Siyasa. Jaridar ta samu sahalewa daga gwamnati, kuma sau da dama ta kan soki Shugaban Nijar Tandja Mamadou. Jaridar mallakar Maman Abou ce, wadda kuma ta mallaki gidan wallafe-wallafen mai zaman kansa mafi girma a Nijar.[1] An ƙaddamar da sigar jaridar ta ɓangaren yanar gizo-(online version) a shekarar 1999.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ A crusading publisher pushes Niger's limits. Jennifer Margulis, The Christian Science Monitor, April 17, 2007.
- ↑ "Le Republicain". Bamako2000.org (in Faransanci). Archived from the original on 24 August 2000.