Lesao Lehohla
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 28 ga Yuli, 1946 (79 shekaru) | ||
| ƙasa | Lesotho | ||
| Karatu | |||
| Harsuna |
Turanci st (mul) | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
Lesotho Congress for Democracy (en) | ||
Archibald Lesao Lehohla (an haife shi a ranar 28 ga watan Yuli 1946) [1] mataimakin Firayim Minista ne kuma Ministan Harkokin Cikin Gida da Tsaron Jama'a na ƙasar Lesotho.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Lehohla a ranar 28 ga watan Yuli 1946 a Mafeteng. A cikin shekarar 1970, Lehohla ya sami digiri na kimiyya daga Jami'ar Botswana, Lesotho da Swaziland (UBLS). A cikin shekarar 1975, ya sami gurbin karatu daga UNESCO don halartar Jami'ar Oxford a fannin ilimin lissafi. Yayin da yake Oxford, Lehohla ya kammala karatun digiri na biyu da kuma Master of Arts. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Yayin halartar UBLS, Lehohla ya kasance mataimakin mai koyarwa daga shekarun 1970 zuwa 1972. Lehohla ya fara koyarwa a Makarantar Sakandare ta Bereng a shekarun 1975 kuma an ƙara masa girma zuwa shugaban makaranta a shekarar 1977. Lehohla ya kasance a matsayin shugaban makaranta har zuwa shekara ta 1993.[2]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An fara zaɓen Lehohla a matsayin ɗan majalisa daga mazaɓar Mafeteng a shekarar 1993 kuma ya zama Ministan Harkokin Cikin Gida [1] a sabuwar gwamnatin Jam'iyyar Basutoland Congress Party. Daga baya ya zama Ministan Sufuri, Wasika da Sadarwa a shekarar 1995. [1] A watan Mayun 1996 ya zama Ministan Ilimi. [3] Ya lashe hukuncin kotu da ya ba shi damar sake tsayawa a mazaɓar Mafeteng a zaɓen shekarar 1998 bayan jam’iyyarsa, Lesotho Congress for Democracy (LCD), ta zaɓi wani ɗan takara, [4] kuma aka sake zaɓe. [1]
Mataimakin Firayim Minista
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 27 ga watan Janairun 2002, an zaɓi Lehohla a matsayin shugaban jam'iyyar Lesotho Congress for Democracy Party. [5] Wannan matsayi na shugaban jam'iyyar ya kai shi ga samun muƙamin mataimakin firaminista daga baya a zaɓen 'yan majalisa na shekarar 2002. [6] An cire Lehohla daga muƙaminsa na Ministan Ilimi kuma a maimakon haka ya zama Ministan Harkokin Cikin Gida da Tsaron Jama'a a cikin watan Nuwamba 2004. [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "The Lesotho MINISTRY OF HOME AFFAIRS and PUBLIC SAFETY, and of PARLIAMENTARY AFFAIRS - Minister's Profile". lesotho.gov.ls. Archived from the original on 1 December 2008. Retrieved 16 November 2016. Cite error: Invalid
<ref>tag; name "Gov" defined multiple times with different content - ↑ Rosenberg, Scott; Weisfelder, Richard F. (2013). Historical Dictionary of Lesotho (2nd ed.). pp. 225–226. ISBN 9780810867956. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Dissension within the Ruling Party". Summary of Events in Lesotho. 3 (2). 1996. Archived from the original on 7 February 2012. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Runup to the General Election". Transformation Resource Center. 1998. Archived from the original on 7 February 2012. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Lehohla is the New LCD Deputy Leader". business.highbeam.com. Archived from the original on 16 November 2016. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Archibald Lesao Lehohla". ibe.unesco.org. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Major Cabinet Reshuffle Announced". Summary of Events in Lesotho. 8 (4). 2001. Archived from the original on 7 February 2012. Retrieved 16 November 2016.