Jump to content

Linda Agnes Auma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Linda Agnes Auma
member of parliament (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Uganda, 
ƙasa Uganda
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa independent politician (en) Fassara

Linda Agnes Auma 'yar siyasa ce kuma 'yar majalisa a Uganda. Ta wakilci al'ummar gundumar Lira a matsayin mace 'yar majalisa a majalisar dokoki ta 11 ta Uganda, wacce ta shiga a kan tikiti mai zaman kanta. [1] Ita ce mataimakiyar shugabar majalisar mata ta ƙasa. Auma ita ce shugabar kwamitin majalisar dokoki kan aikin gona, masana’antar dabbobi da kifaye; Ita kuma ita ce Sakatariyar Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Majalisun Mata ta Uganda (UWOPA) da Ƙungiyar Majalisar Lango.

A baya ta yi aiki a matsayin Hakimar gundumar Amuru inda ta ajiye muƙamin a shekarar 2021 ta shiga majalisa.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Auma ɗiya ce ga marigayi Manjo Janar David Oyite Ojok, babban hafsan hafsoshin Sojin ƙasa na Uganda (UNLA) a lokacin shugabancin Dr Apollo Milton Obote na biyu. [2] [3]

Auma mahaifinta ya rasu tana da shekara 2 a duniya. Oyite Ojok ya halaka ne a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar 2 ga watan Disamba, 1983, ta shiga aikin tantance ci gaban kungiyar ‘yan tawaye, National Liberation Army (NRA) ƙarƙashin jagorancin Yoweri Kaguta Museveni, wanda daga baya ya kwace mulki a shekarar 1986. [2]

Ita ma Auma ta rasa mahaifiyarta tun tana da shekara 8, wanda hakan ya sa ta zama marainiya gaba ɗaya, kuma yarintarta ta kasance cikin talauci da kunci. Auma ta tafi makaranta tare da taimakon masu hannu da shuni, kuma ta haifi ‘yarta ta fari tana da shekara 16.

Tana da shekaru 26. Auma a matsayin mahaifiyar yara 2 ta koma makaranta don kammala karatunta na O'level kuma shugaban ƙasar Yoweri Museveni ya biya kuɗin makarantar, wanda ya yi yaki tare da mahaifinsa a UNLA don kawar da Shugaba Amin [2] [3]

Daga nan ta yi kwas din satifiket a fannin lissafi sannan ta yi difloma kan harkokin kasuwanci sannan ta yi digiri na farko a fannin kasuwanci. [2]

Auma ta shiga siyasa ne ta hanyar tsayawa takara kuma ta zama shugabar matasan ƙaramar hukumar Lira a ƙarƙashin majalisar matasa ta ƙasa, daga baya kuma a shekarar 2006 aka zaɓe ta a matsayin kansila ga matasa a sashin tsakiya na ƙaramar hukumar Lira. [2]

A cikin shekarar 2016 ta nemi kujerar MP na Mata a Lira a kan tikitin jam'iyyar Resistance Movement na ƙasa amma ta sha kashi a zaɓen fidda gwani. Joyce Ongom ta jam'iyyar Uganda People's Congress (UPC) ce za ta lashe kujerar 'yar majalisar.

Bayan babban zaɓen Uganda na shekarar 2016, shugaba Museveni ya naɗa Auma a matsayin RDC na gundumar Amuru. [4]

A ci gaba da zaɓen ƙasar Uganda na shekarar 2021, Auma ta lashe Florence Angina a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar NRM, amma nasarar da ta samu ya ci tura bayan sake ƙidaya kuri'u. [5]

An ayyana Florence Angina a matsayin mai riƙe da tutar jam’iyyar NRM a matsayin mace ‘yar majalisar wakilai ta Lira, lamarin da ya sa Auma tsayawa takara a matsayin ‘yar takara mai zaman kanta kuma ita ce ta yi nasara a babban zaɓen ƙasar. [6] [5]

A majalisar dokokin Uganda, Auma tana aiki a kwamitin masana'antun dabbobi da kamun kifi, kakakin kungiyar majalisar dokokin Lango da kuma sakatariyar yaɗa labarai ta kungiyar 'yan majalisar dokokin Uganda (UWOPA). [7] [8]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Aumas 'yar fari ce ga Shakila Among Mwenyi ta lashe kambin Miss Lira a shekarar 2017. Ta kuma kasance fuskar Tarihin Al'adu na Lango kuma an naɗa ta Miss Tourism Northern Region a shekarar 2020. Shakila Among kuma tana wakiltar matasa na Lira a majalisar birni ta Lira a matsayin Mata mai ba da shawara.[2] Shakila ita ce Mataimakinyar Kakakin Majalisar Birnin Lira na yanzu.

  1. Tushabe, Nasa (2021-01-18). "Full List of Winners and Losers of 2021 Member of Parliament Elections". The Pearl Post (in Turanci). Archived from the original on 2022-03-08. Retrieved 2022-04-04.
  2. 1 2 3 4 5 6 Reporter, Independent (2021-02-04). "Tragic childhood shaped Agnes Auma's Achy journey to parliament". The Independent Uganda (in Turanci). Retrieved 2022-04-04.
  3. 1 2 "Amin's granddaughter salutes Museveni for being a father figure". Nile Post (in Turanci). 2021-04-26. Retrieved 2022-04-04.
  4. Eyalama (2018-06-19). "Full List: President Museveni Releases Revised List OF RDC's Nullifying The 15th June List". Uganda News, Politics, Entertainment,Business and Special Reports (in Turanci). Archived from the original on 2022-05-27. Retrieved 2022-04-04.
  5. 1 2 Reporter, Independent (2020-10-03). "Former Lira woman NRM flag winner rejects fresh tally results". The Independent Uganda (in Turanci). Retrieved 2022-04-04.
  6. "High court dismisses election petition filed against Lira Woman MP". The Independent Uganda (in Turanci). 2021-08-25. Retrieved 2022-04-04.
  7. "UWOPA Elects New Executive for the 11th Parliament of Uganda | UWOPA". uwopa.or.ug. Archived from the original on 2022-03-13. Retrieved 2022-04-04.
  8. "Sarah Opendi to Advocate for Enacting of Gender Related Laws as UWOPA Chairperson". East News (in Turanci). 2021-11-02. Retrieved 2022-04-04.