Jump to content

Linda MacDonald (mai fafutuka)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Linda MacDonald 'yar gwagwarmayar Kanada ce game da azabtarwa da ba na gwamnati ba, keta haƙƙin ɗan adam da aikata laifuka. [1]

An haife ta a Charlottetown,[2] MacDonald tsohuwar ma’aikaciyar jinya ce dake zaune a Nova Scotia, Kanada, kuma ita ce hadaddiyar kafa kungiya mai suna Persons Against Non-State Torture — wani kamfen na kare hakkin dan Adam wanda take daukar nauyinsa da kanta.[3][4][5] MacDonald ta yi aiki a asibitoci, kiwon lafiya na jama’a, da kuma a matsayin mai tsara kulawa ga masu bukatar taimakon gida.[6] Ita mai hada-hadar sadarwa ce, mai koyarwa, mai bincike, marubuciya kuma memba ce a kungiyar NGO Alliance on Crime Prevention and Criminal Justice, Nation Council of Women Canada da ACUNS.[7] [8]

Ta sami RN a asibitin Victoria General, digiri na farko na Nursing a Jami'ar Dalhousie da kuma digiri na Masters na Ilimi a Jami'an St. Mary duk a Halifax, Nova Scotia, Kanada.

An gabatar da MacDonald a shirin rediyo na ‘yan mata masu fafutuka na Robin Morgan' mai suna WMC Live. Tana aiki tare da Jeanne Sarson a matsayin masu fafutukar kare hakkin ‘yan mata da mata waɗanda suka sha wahala daga Azabtarwa ta Hannun Ƙungiyoyi Marasa Gwamnati (NST).

  1. "Speaking Out Against Non-State Torture: Linda MacDonald and Jeanne Sarson - Raise the Hammer". raisethehammer.org. Retrieved 2019-03-29.
  2. "Jeanne Sarson and Linda Macdonald speak out against Non-State Torture". FiLiA (in Turanci). Retrieved 2019-03-29.
  3. "Speaking Out Against Non-State Torture: Linda MacDonald and Jeanne Sarson - Raise the Hammer". raisethehammer.org. Retrieved 2019-03-29.
  4. "Macdonald, Linda". ACUNS (in Turanci). 2018-12-10. Archived from the original on 2019-03-29. Retrieved 2019-03-29.
  5. MacIvor, Angela; Allen, Susan (May 30, 2014). "Woman alleging torture at parents' hands felt like a 'thing' for years". CBC (in Turanci). Retrieved 2019-03-29.
  6. "Episode138.mp3".[permanent dead link]
  7. "Jeanne Sarson and Linda Macdonald speak out against Non-State Torture". FiLiA (in Turanci). Retrieved 2019-03-29.
  8. "Champions for the cause". www.canadian-nurse.com (in Turanci). Retrieved 2019-03-29.