Jump to content

Lissafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lissafi
academic discipline (en) Fassara da academic major (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na natural science (en) Fassara
Bangare na formal science (en) Fassara da exact science (en) Fassara
Amfani ilmi, mathematical modelling (en) Fassara, Injinia., finance (en) Fassara da computation (en) Fassara
Fuskar mathematics education (en) Fassara
Suna a harshen gida μᾰθημᾰτικά
Gajeren suna maths
Is the study of (en) Fassara mathematical object (en) Fassara
Hashtag (mul) Fassara math, mathematics da maths
Has characteristic (en) Fassara mathematical beauty (en) Fassara, formalization (en) Fassara da har’abada
Tarihin maudu'i tarihin lissafi da bayanan lissafi
Gudanarwan masanin lissafi da mathematics student (en) Fassara
WordLift URL (en) Fassara http://data.thenextweb.com/tnw/entity/mathematics
Stack Exchange site URL (en) Fassara https://math.stackexchange.com
Lissafi kenan
Lissafi

Lissafi ko kuma nazarin ƙidaya wani fanni ne na ilimi wanda yake taimakawa ɗan Adam yin ƙidaya da sanin yawan abubuwa da kuma sanin tsarin yadda abubuwa suke idan an canza su ta wata suffar. Ko kuma Ilimi ne na fasaha wanda ake koyan yadda ake tsare-tsare, zane-zane da kuma ƙere-ƙere ta hanya mai sauki.

Shi lissafi ya rabu kashi biyu: Lissafi wani fannin ilimi ne da ya shafi nazarin ƴaƴan ƙididdiga adadi, sarari, tsari, yanayi da sauyi. Ana amfani da ilimin lissafi a ɓangarori da dama kamarsu; kimiyya, kanikanci, likitanci, da kimiyyar zaman takewa. Amfanin ilimin lissafi a waɗansu lokuta shike haifar da sabbin rassa a fannin kamar lissafin ƙididdiga kuma masana lissafi suna anfani da lissafi tsagwaran sa, ba don wani dalili ba, ba wani abu dazai iya bayyana maka wannan lissafi ne na amfani ko kuma a'a ba.

  • lissafin zane
    lissafin numbobi
    (1) akwai lissafi na lambobi, kasafi da ƙidaya wato (haɗawa, rubawa, ninkawa da kuma fiddawa) wadda ake ƙira Aljebra.
  • (2) Akwai kuma lissafi na zane-zane na muhalli, ƙirƙire-ƙirƙire da sauransu da ake ƙira Geometri.

Geometri tana taimakawa wajen sanin suffar abu: wato tsawonsa, faɗinsa, girmansa da yawansa. Tana taimaka mana a taƙaice a cikin fannin gini, ƙira da kuma suffur.

lissafin statistic kenan

Ana yin lissafi kafin ayi wani abu domin a san me nene sakamakon abun idan ya faru wannan ɓangaren na lissafi ana kiransa Kasafi wato "statistics" a turance. A cikin wannan fanni na Kasafi a kan haɗa gamayyar abubuwa a yi nazari akan sakamakon da za su bayar idan anyi wani abu akan su ta hanyar anfani da alƙalamomin da suke a cikin su.

Lissafi

Sanin asalin ilimin lissafi abu ne mai wahalar gaske amma an fara ganin lissafai masu wahala ne akusan shekarata 3000 kafin bayyanar Annabi Isa (300 MD) a lokacin [[babila]] da Misra suka fara lissafin ƙirga da lissafin awo, domin haraji, kasuwanci, gine-gine, tsare-tsare da kuma iimin taurari mafi daɗewar rubutun da aka samu akan lisafi an same sune a ƙasa-shen  Mesofotamiya and misra waɗanda aka rubuta su a kimani shekaru 2000–1800 kafin haihuwar annabi Isah Ya fara faruwa ne a lokacin ƙarni na shida yayin da pathogares (daya daga cikin masanan lissafi na wancen lokacin) da ɗalibansa suka fara nazarin lissafi amatsayin darasi tareda masana lissafin Girka shekaru 3000 kafin zuwan annabi Isah. Masanin lissafin nan Ecluid shine ya samar da wata hanyar lissafi da akeƙira da turanci (axiomation). Wanda har yau ana amfani dashi.