Lowila CD Oketayot
![]() | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 24 Disamba 1969 (55 shekaru) | ||
ƙasa | Uganda | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Opette Primary School (en) ![]() Cibiyar Horar da Aikin Gona ta Bukalasa Kitgum High School (en) ![]() Sacred Heart School (en) ![]() Jami'ar Makerere | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Manoma | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
National Resistance Movement (en) ![]() |
Lowilo CD Oketayot (an haife shi 24 Disamba 1969) ƙwararriya kuma masaniya a fannin aikin gona, 'yar siyasa, kuma 'yar majalisa.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Lowilo CD Oketayot (an haife ta a ranar 24 ga watan Disamba 1969) ƙwararriya masaniya a fannin aikin gona, 'yar siyasa, kuma 'yar majalisa. Ita 'yar majalisar dokokin Uganda ce mai wakiltar mutanen gundumar Pader a matsayin wakiliyar mata ta gunduma tun a shekarar 2011. [2] Ita mamba ce a Jam'iyyar National Resistance Movement (NRM), [3] jam'iyyar a jagorancin siyasa a Uganda [4] ƙarƙashin jagorancin Yoweri Kaguta Museveni, shugaban Jamhuriyar Uganda.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Oketayot ta fara karatun firamare ne daga makarantar firamare ta Oppete Archived 2024-04-16 at the Wayback Machine a shekarar 1982 inda ta yi jarrabawar kammala firamare (PLE) a shekarar 1982, ta karanci matakin O-level a Sacred Heart Secondary School Gulu inda ta yi satifiket ɗin ta na Uganda (UCE) a shekarar 1986, ta shiga makarantar sakandare ta Kitgum don samun karatunta na matakin A-level sannan ta kammala karatun digiri na uku a Uganda (199).[5] Ta yi karatun digiri a fannin noma daga kwalejin aikin gona ta Bukalasa a shekarar 1994 sannan ta yi difloma a fannin aikin gona daga baya a wannan cibiyar a shekarar 1996. Ta shiga Jami’ar Makerere inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin aikin gona a shekarar 2007 sannan ta kara digiri na biyu a fannin tattalin arzikin noma daga jami’ar Makerere a shekarar 2015.[6]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Oketayot ta kasance memba na majalisar dokokin Uganda tun a shekarar 2011, [7] ta kasance manajar aikin gona ZOA Uganda daga shekarun 2009 zuwa 2010 kuma mai kula da aikin gona ZOA Uganda daga shekarun 2008 zuwa 2009. [8] Ta yi aiki a matsayin jami'ar aikin kula da ilimin kula da cutar kanjamau (ACET) Uganda daga shekarun 1996 zuwa 2001, kuma ta yi aiki a matsayin jami'ar shirin ACET Uganda daga shekarun 2001 zuwa 2003.[9]
A majalisa ta 10, ta zama shugabar kwamitin kula da masana'antar dabbobi da kamun kifi.[10] kuma memba ce ta kwamitin kasuwanci. [11] Ta kuma wakilci yankin arewa a kungiyar mata 'yan majalisar dokokin Uganda (UWOPA). [12]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Henry, Lutaya (2018-08-10). "Agriculture committee strives to restore sector to rightful place". The sunrise. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "Find an mp". Parliament of the republic of uganda. Archived from the original on 2021-11-30. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "Parliament of Uganda, members of the 10th parliament". Parliament of uganda.
- ↑ "National resistance movement". NATIONAL RESISTANCE MOVEMENT. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ Henry, Lutaya (2018-08-10). "Agriculture committee strives to restore sector to rightful place". The sunrise. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ Henry, Lutaya (2018-08-10). "Agriculture committee strives to restore sector to rightful place". The sunrise. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "Parliament of Uganda members of the 10th parliament". Parliament of uganda. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "Lowila Oketayot". ISSUU. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ Henry, Lutaya (2018-08-10). "Agriculture committee strives to restore sector to rightful place". The sunrise. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ Henry, Lutaya (2018-08-10). "Agriculture committee strives to restore sector to rightful place". The sunrise. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "Business committee". Parliament of the republic of Uganda. Retrieved 2020-04-06.
- ↑ "UWOPA executive 10th parliament". UGANDA WOMEN PARLIAMENTARY ASSOCIATION. Archived from the original on 2020-04-06. Retrieved 2020-04-06.