Luísa Rogério
Maria Luísa Rogério 'yar jaridar ƙasar Angola ce.[1] Ta kuma yi aiki a matsayin shugabar Hukumar Kula da Ka'idojin Kasuwanci ta ƙasar [1] kuma ta kasance memba na Kwamitin Zartarwa na Tarayyar 'Yan Jarida ta Duniya tun daga shekarar 2019. [2][3][4]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Rogerio ta fara aiki a aikin jarida a ƙarshen shekarar 1980s. [1]
A shekarar 1999 da 2000, ta kasance babbar daraktar na kungiyar AMUJA, kungiyar mata ‘yan jarida a Angola. [5] Tsakanin shekarun 2004 zuwa 2015, Rogerio ita ce babbar sakatariya na kungiyar 'yan jarida ta Angolan. [3] A shekarar 2013, an zabe ta mataimakiyar shugabar kungiyar 'yan jarida ta Afirka. [3] A cikin shekarar 2019, an naɗa ta shugabar sabuwar ƙirƙira ta Comissão da Carteira e Ética Profissional (CCE; Turanci: Card and Professional Ethics Commission), wata ƙungiyar doka mai zaman kanta wacce ke baiwa 'yan jaridu a Angola, mai sa ido kan ayyukan 'yan jarida, da magance cin zarafi na ɗabi'a a aikin jarida. [2]
Rogerio ta ba da labarai iri-iri na gida da waje, ciki har da yarjejeniyar Lusaka da babban zaɓe na shekarar 2018 DRC. [1] [3] Ta rubuta Jornal de Angola da Rede Angola.
Ta ci gaba da yin tofa albarkacin bakinta game da batun cece-kucen 'yan jaridu a Angola tare da bayar da shawarwarin 'yancin 'yan jarida. [6] [7] [8] [9] Ta kuma taimaka wa 'yan jaridun ƙasashen waje su yi aiki a ciki da kuma bayar da rahoto daga Angola. [10]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 "Angola: "Covering conflict zones came so naturally that before I knew it I was already there"". International Federation of Journalists (in Turanci). 2023-03-08. Retrieved 2024-12-22. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":0" defined multiple times with different content - 1 2 "Jornalistas angolanos têm agora órgão fiscalizador da ética profissional". Voice of America (in Harshen Potugis). 2019-10-31. Retrieved 2024-12-22. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":1" defined multiple times with different content - 1 2 3 4 Luamba, Manuel (2019-06-27). "Luísa Rogério, jornalista angolana de projeção internacional". Deutsche Welle (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":2" defined multiple times with different content - ↑ "Angola sobe, restantes PALOP descem no Índice Mundial da Liberdade de Imprensa". RFI (in Harshen Potugis). 2024-05-03. Retrieved 2024-12-22.
- ↑ Victoria, Alvaro (2020-10-31). "″Que linha editorial é esta que privilegia os interesses de quem está no poder?″ - Luísa Rogério, presidente da CCE". Novo Jornal (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22.
- ↑ "AFS - Luísa Rogério: "O aumento da censura é extremamente preocupante"". Voice of America (in Harshen Potugis). 2014-05-02. Retrieved 2024-12-22.
- ↑ Zamba, Leonel (2022-12-16). "«O que está a acontecer aqui é um sinal claro de que o exercício da profissão é cada vez mais perigoso» - Luísa Rogério, presidente da CCE". Novo Jornal (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22.
- ↑ Cascais, António (2011-05-16). "Angola nova proposta de lei poderá violar liberdade de informação". Deutsche Welle (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22.
- ↑ José, Manuel (2022-10-13). "Jornalistas angolanos admitem sair às ruas em protesto contra cerco à sua actividade". Voice of America (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22.
- ↑ José, Manuel (2012-08-22). "Angola: CNE adopta regras problemáticas para credenciamento de jornalistas". Voice of America (in Harshen Potugis). Retrieved 2024-12-22.
- ↑ "Angola Fala Só: Bilhete de Identidade de Luísa Rogério". Voice of America (in Harshen Potugis). 2014-05-01. Retrieved 2024-12-22.