Jump to content

Lucie Ablawa Sessinou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lucie Ablawa Sessinou
Rayuwa
ƙasa Benin
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, mayor (en) Fassara, Malami da entrepreneur (en) Fassara

Lucie Ablawa Sessinou 'yar siyasar Benin ce kuma magajiyar garin Kétou. An zaɓe ta a kan tikitin jam'iyyar siyasa ta Benin Progressive Union a zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2020. A watan Yulin 2018, ta zama shugabar cibiyar zaɓaɓɓun kansilolin mata a Benin.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Lucie Ablawa Sessinou ta zama magajin garin Kétou na farko a shekara ta 2003 a lokacin wa'adin mulkin farar hula na farko a Benin bayan zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2002. Ta rasa muƙamin ne a shekarar 2008 a lokacin zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2008. [1] [2] [3]

Tsohuwar malamar da ta zama ‘yar kasuwa, Lucie Ablawa Sessinou ta ba da shawarar shigar da matan Benin cikin harkokin tafiyar da harkokin birane da gudanar da harkokin ƙasa. Ta kafa cibiyar sadarwa na zaɓaɓɓun kansilolin mata a Benin kuma ta kasance shugabar ta har zuwa watan Yuli 2018. [4] [5] [6]

An sake zaɓen ta a matsayin magajin garin Kétou a zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2020, an kaddamar da ita a ofis a ranar Asabar, 6 ga watan Yuni, 2020, a wani bikin da Shugaban Ma'aikatar Filato, Daniel Valère Setonnougbo ya jagoranta. [7] [8] [9] [10]

  1. "Mairie de Kétou: Le come-back de Lucie Sessinou". La Nation Bénin. 2020-06-06. Archived from the original on 2021-06-07. Retrieved 2021-06-07.
  2. "La Convention de Coopération entre Vauréal et Kétou". gsvaureal-ketou.e-monsite.com. Retrieved 2021-06-07.
  3. "Le maire Lucie Sessinou invite les populations à jouer leur partition pour booster le développement de Kétou". Agence Bénin Presse. Retrieved 2021-06-07.
  4. "BÉNIN : LUCIE SESSINOU ÉVOQUE LA BONNE GOUVERNANCE AU NIVEAU DÉCENTRALISÉ - First Afrique Mag". First Afrique Mag. 2021-03-20. Archived from the original on 2021-06-07. Retrieved 2021-06-07.
  5. "Réseau des femmes élues conseillères communales du Bénin : Lucie Sessinou installe les nouveaux membres du bureau". Le Portail Info. 2021-01-19. Archived from the original on 2021-06-07. Retrieved 2021-06-07.
  6. "LUCIE SESSINOU, maire de Kétou approuve la gouvernance - First Afrique Mag". First Afrique Mag. 2021-03-20. Archived from the original on 2021-06-07. Retrieved 2021-06-07.
  7. "Kétou : Lucie Sessinou prends la Mairie". Le Leader Info Benin. 2020-06-06. Retrieved 2021-06-07.[permanent dead link]
  8. "Etat de la commune de Kétou:Le diagnostic sans appel du maire Lucie Sessinou". La Nation Bénin. 2020-12-03. Archived from the original on 2021-06-07. Retrieved 2021-06-07.
  9. "Lucie Sessinou élue maire de Kétou". 24haubenin.info. 2020-06-06. Retrieved 2021-06-07.
  10. "Deux femmes élues maires dans le Plateau: L'effet d'une transformation sociale". Acotonou.com. Retrieved 2021-06-07.