Ludy Kissassunda
1995 - 2004 | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
N'zeto (en) | ||
| ƙasa | Angola | ||
| Mutuwa |
Setúbal (mul) | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Portuguese language | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | MPLA | ||
Janar João Rodrigues Lopes, wanda aka fi sani da sunan sa Ludy Kissassunda (27 Satumba shekara ta alif 1932 - 6 Janairu 2021) Janar ne kuma ɗan siyasa na Angola.[1] An haife shi a shekara ta 1932 a N'zeto, lardin Zaire, ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a lokacin yakin 'yancin kai na kasart Angola da yakin basasar Angola, yana da muhimmiyar rawa tare da sake tsara sojojin, da kuma dukkanin kayan aiki na rundunar 'yantar da jama'ar Angola, wanda daga bisani za ta zama rundunar sojojin Angola ta FAPLA. [2]
A lokacin aikinsa na siyasa, ya kasance memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar People's Movement for the Liberation of Angola (MPLA), kasancewarsa ɗaya daga cikin makusantan Agostinho Neto. [3] Shi ne wanda ya kafa kuma darekta na Sashen Watsa Labarai da Tsaro na ƙasar Angola (DISA), hukumar leken asiri ta MPLA (da kuma Angola), daga shekarun 1975 zuwa 1979.[2] Ya kuma kasance gwamnan lardin Malanje daga shekarun 1980 zuwa 1986, da na lardin Zaire daga shekarun 1995 zuwa 2004.[4]
Kissassunda ya mutu a ranar 6 ga watan Janairu 2021 a Setúbal, Portugal. [3] An binne shi a makabartar Alto das Cruzes a Luanda.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1 João Lopes / Ludy Kisasunda. ATD. 2023.
- ↑ 2.0 2.1 ""O País tem uma falta de memória histórica generalizada" - Maria Helena, viúva de Iko Carreira". Club-K. Archived from the original on 2019-09-05. Retrieved 2019-07-20.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Mensagem de Condolências Pelo Falecimento do Camarada Rodrigues João Lopes «Ludy Kissassunda»". MPLA Bureau Político. 8 January 2021. Archived from the original on 8 September 2021. Retrieved 20 August 2024.
- ↑ General Ludy Kissassunda é sepultado no Alto das Cruzes Archived 2021-09-06 at the Wayback Machine. Jornal de Angola. 15 de janeiro de 2021.