Jump to content

Lukas Podolski

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lukas Podolski
Rayuwa
Cikakken suna Łukasz Józef Podolski
Haihuwa Gliwice (en) Fassara, 4 ga Yuni, 1985 (39 shekaru)
ƙasa Jamus
Poland
Ƴan uwa
Mahaifi Waldemar Podolski
Mahaifiya Krystyna Podolska
Karatu
Harsuna Jamusanci
Polish (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da marubucin labaran da ba almara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Germany national under-17 association football team (en) Fassara2001-200262
  Germany national under-18 football team (en) Fassara2002-200374
  Germany national under-19 football team (en) Fassara2003-200336
  1. FC Köln (en) Fassara2003-200320
  1. FC Köln (en) Fassara2003-20068146
  Germany national under-21 football team (en) Fassara2004-200450
  Germany men's national association football team (en) Fassara2004-201713049
  FC Bayern Munich2006-20097115
  FC Bayern Munich II (en) Fassara2007-200820
  1. FC Köln (en) Fassara2009-20128833
Arsenal FC2012-20156019
  Inter Milan (en) Fassara2015-2015171
  Galatasaray S.K. (en) Fassara2015-ga Yuni, 20175620
Vissel Kobe (en) Fassaraga Yuni, 2017-ga Janairu, 20205215
Antalyaspor (en) Fassaraga Janairu, 2020-ga Yuni, 2021406
  Górnik Zabrze (en) Fassaraga Yuli, 2021-
 
Muƙami ko ƙwarewa wing half (en) Fassara
Mai buga tsakiya
Lamban wasa 10
Nauyi 83 kg
Tsayi 182 cm
Kyaututtuka
Imani
Addini Cocin katolika
IMDb nm1889144
lukas-podolski.com
Lucas Podolski
Lukas
Lukas
Lukas

Lucas Podolski(an haifeshi ranar hudu 4 ga watan yuni shekarar alif dari tara da tamanin da biyar miladiyya 1985) dan kasar Jamus ne kuma kwararren dan wasa ne wanda yake buga wurin kai farmaki wato gaba, ko kuma yakan buga tsakiya amma ta kai hari wato dan tsakiya mai sabka gaba a kulob din Eatrakslasa a Gornik zabrze. An haifeshi a garin Gilwise a kasar Poland kuma ya wakilci kasar jamus a wasanni da dama. Dan wasa ne mai basira, ga karfi ga saiti da kuma karfin buga kwallo. Dan wasa ne da ya kware sosai wajan kai farmaki musamman a gefen hagu.

Lukas Podolski
lukas
Podolski
lukas

Podolski ya jona kungiyar Koln a shekarar alif 1999 inda ya shiga cikin babbar kungiyar a shekarar 2003 inda ya buga wasanni guda 81 daga bisani kuma ya canza sheka zuwa kungiyar Bayern Munich.

lukas

A kungiyar Bayern Munich, dan wasan ya lashe gasar Bundesliga da kuma DFB - Porkal har sau biyu 2 a shekarar 2008. Podolski ya koma kungiyar sa ta baya wato koln a 2009, daga baya ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallan kafa ta Arsenal a shekarar 2012 inda yaci gasar F. A Cup a shekarar alif 2014. Sai kuma yaje aro kungiyar kasar Italiya wadda ke buga lig din Serie a wato kungiyar kwallan kafa ta Inter Milan a watan Junairu a shekarar alif 2015 sai kuma ya sa kwantiragin wata takwas da kungiyar Galatasary a shekarar alif 2016.

Dan wasan ya samu dama har guda biyu wajan bugama kasashe har guda biyu wasa, da kasar Jamus da kuma Poland. Ta fannin kakan sa da aka haifa a kasar Jamus, tanan ya samu lasisin buga ma Jamus kwallo.

Kingin kiris dan wasan ya koma kungiyar dake Polish amma abin be yiyuba domin a soke komawar sai kocin Polish din mai suna Pawel Jenas a shekarar 2003. Sannan tun tuni ya bayyana a kasar Jamus inda ya wakilci kungiyar tun yana karamin yaro.

Bayan bayyanar shi ta farko a babbar kungiya a shekarar alif 2004, dan wasan yayi zamani mai kyau tare da kungiyar kasar Jamus. Yana daya daga cikin jerin yan wasan da suka buga gasanni har guda bakwai inda ya samu damar lashe kofin duniya baki daya wanda aka bugashi a shekarar alif 2014.

Dan wasan yana daya daga cikin yan wasan da sukafi kowa doka wasanni a kasar Jamus inda ya buga wasanni guda dari da talatin wanda hakan ya bashi damar shiga cikin jerin yan wasan da suka fi kowa buga wasanni a kasar inda yazo lamba na daya da yafi kowa buga wasanni a kasar, sannan kuma ya samu damar jefa kwallaye guda 49.

A ranar 29 ga watan Mayu 2013, dan wasan yaci kwallo mai sauri a raga cikin dakiku kadan inda ya jefa kwallo a raga cikin sakanni tara kacal wasan da ya wakilci kasar Jamus inda yakafa tarihi da wannan kwallan da ya zura inda suka fafata da kasar Eduardo inda suka lallasasu daci 4-2. Sai kuma daga baya dan wasa mai suna Florian Witz ya karya tarin dan wasan.

Lukas Podolski

Dan wasan ya aje ma kasar Jamus kwallo a shekarar 22 March 2017 inda yaci kwallo wadda taba kasar tashi nasara wasan da suka fafata da kasar Ingila inda wasan ya tashi 1-0

Lukas Podolski

Poldolski yanada karfi da zai buga kwallo da karfi taje inda yakeso. Idan ya buga kwallo takan iya kai nisan 100mph. Shahararren Babban koci mai suna Arsen Wenger ya bayyana dan wasan a matsayin dan kwallo da yake zura kwallo a raga ta ko wane hali. A yanda yace, dan wasan yana daya daga cikin yan wasa mafi iya zura kwallo a raga da ban taba ganin irinsu ba. A yanda yace, indai kana neman dan kwallo da ya san abinda yake, kuma wanda ze zura ma kwallo a kowane hali to ka nemo shi. A lokacinshi yana daya daga cikin yan wasa masu gudu kuma yana cikin yan wasan da suka fi kowa iya zura kwallo a raga. Sannan yana cikin yan wasan da suka fi kowa karfin buga kwallo a raga.