Jump to content

Luzia Inglês Van-Dúnem

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Luzia Inglês Van-Dúnem
Member of the National Assembly of Angola (en) Fassara


District: National Constituency of Angola (en) Fassara
Member of the National Assembly of Angola (en) Fassara


District: National Constituency of Angola (en) Fassara
Member of the National Assembly of Angola (en) Fassara


District: National Constituency of Angola (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna Inglês
Haihuwa Luanda, 11 ga Janairu, 1948 (77 shekaru)
ƙasa Angola
Ƴan uwa
Abokiyar zama Afonso Van-Dunem (en) Fassara
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar
Imani
Jam'iyar siyasa People's Movement for the Liberation of Angola (en) Fassara

Luzia Pereira de Sousa Inglês Van-Dúnem (an haife ta a ranar 11 ga watan Janairu 1948) 'yar siyasa ce ta Angola, mai ƙare 'yancin mata kuma ƙwararriya a fannin sadarwa na soja. Ita mamba ce a Majalisar Dokokin Angola, a matsayinta na memba na Popular Movement for the Liberation of Angola (MPLA).

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Van-Dúnem a Luanda, Angola, a ranar 11 ga watan Janairu 1948 kuma 'yar ministar Methodist, Guilherme Inglês. A cikin shekarar 1961 sojojin mulkin mallaka suka kashe Inglês bayan boren 15 ga watan Maris. [1] Mahaifiyarta ta rasu jim kaɗan bayan haka kuma ita da yayyenta mata sun shiga Movimento Popular de Libertação de Angola (MPLA; People's Liberation Movement of Angola). [2] Daga shekarun 1964 zuwa 1967 ta kasance a Kinshasa da Brazzaville tare da MPLA; a Brazzaville, ta gudanar da horon soja. [2] A shekarar 1968 ta tafi zuwa Tarayyar Soviet don samun horo a harkokin sadarwa. [2] A shekarar 1973, ta zama shugabar tashar sadarwa a Cassamba. [1] A lokacin Yaƙin ƴancin kai na Angola, Van-Dúnem ta kasance mai watsa shirye-shiryen rediyo a yankunan siyasa na soja na 2 da na 3. [3] Daga shekarun 1976 zuwa 1991 ta kasance mai kula da babban kwamandan rundunar sojin ƙasar Angola. [1] [2]

Van-Dúnem ta auri Afonso Van-Dúnem M'binda, tsohon jakadan Angola a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) kuma sun haifi 'ya'ya huɗu. [1] Yayin da aka naɗa M'binda jakada a cikin shekara ta 1991, Van-Dúnem kuma ta yi aiki da Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ta jagoranci kungiyar matan Afirka. [3] [1] A cikin shekarar 1999, an zaɓi Van-Dúnem Sakatare-Janar na Organização da Mulher Angolana (OMA), wanda shine reshen mata na jam'iyyar siyasa, People's Movement for the Liberation of Angola (MPLA), kuma an sake zaɓen ta a shekara ta 2005. [1] [4] [5] A shekarar 2008 aka zaɓe ta a majalisar dokokin Angola, a zaɓen farko tun 1992. Mace ce mai fafutukar kare hakkin mata, ta kasance babbar mai bayar da goyon bayan ɓullo da dokar da ke nufin cewa akalla kashi 30% na mutanen da ake son shiga cikin jerin jam’iyyun siyasa su zama mata. [2] Hakan ya kara yawan wakilcin mata a majalisar dokokin ƙasar kuma a zaɓen shekara ta 2008, mata sun kai kashi 36% na mambobin da aka zaɓa. [2]

A shekarar 2014, ta zama mace ta farko 'yar Angola da ta samu karin girma zuwa muƙamin Janar-Janar na Rundunar Sojin Angola; Shugaban ƙasar José Eduardo dos Santos ne ya zartar da wannan ci gaba. [6] [4] A babban zaɓe na shekarar 2017, ƙungiyar zaɓe ta ƙasa ta zaɓi Van-Dúnem mataimakiya daga Angola. [3] A shekarar 2020 aka zaɓe ta Sakatariyar Yanki na Kungiyar Mata ta Pan-African Women’s Organisation (OPM). [7]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 "Luzia Inglês "Inga", SG da OMA". CLUB-K ANGOLA - Notícias Imparciais de Angola (in Harshen Potugis). Retrieved 2021-01-12.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :3
  3. 3.0 3.1 3.2 "Perfil - Assembleia Nacional". www.parlamento.ao. Retrieved 2021-01-12.
  4. 4.0 4.1 "Luzia Inglês". Rede Angola - Notícias independentes sobre Angola. Retrieved 2021-01-12.
  5. "ANGOLA: LUZIA INGLÊS VAN-DÚNEM REELEITA SECRETÁRIA-GERAL DA OMA". www.angop.ao. Retrieved 2021-01-12.
  6. "Presidente angolano promovou uma mulher a oficial general - DN". www.dn.pt (in Harshen Potugis). Archived from the original on 2021-01-16. Retrieved 2021-01-12.
  7. "LUZIA INGLÊS TAKES ON CHALLENGES AT OPM". www.angop.ao. Retrieved 2021-01-13.