Mahaman Shata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Alhaji Mamman Shata, ya rasu a shekarar 1998. ya na da shekara fiye da 70 a lokacin mutuwar sa. Mamman Shata na daya daga cikin mawwakan gargajiya da aka fi sani a kasashen Hausa da afirka, kai harma da duniya.Ya kasan ce masha hurin Mawaki,domin a fagen wakarsa ya shahara. Kasan cewar ya kasance a cikin waka ba abin da bazaiwa waka ba. Shi yasa ake masa kirari da SHATA IKON ALLAH.KUMA MAHADI MAI DOGON ZAMANI.

Yan Arewa Ku Bar Barci na daya daga cikin wakokin sa.

Shata: Yan Arewa Ku Bar Barci, Najeriyarmu Akwai Dad'i 'yan arewa a bar barci, Najeriyarmu, akwai dad'i. To!

'Yan Amshi: A'a, 'yan arewa a bar barci, Najeriyarmu, akwai dad'i.

Shata: K'asar Afuruka, bak'ar fata, K'asar Afruruka, bak'ar fata, In ka yi yawo ciki nata, Duk ba kaman Najeriya, gidan dad'i, Najeriya k'asar farin jini, Najeriya ce gidan dad'i, Balle arewa uwar dad'i. To!

'Yan Amshi: A'a, 'yan arewa a bar barci, Najeriyarmu, akwai dad'i.

Shata: Oh, northerners stop sleeping, Our Nigeria, it's a pleasant place. Source: [1]