Mai Girma Vladimir
Vladimir I Sviatoslavich ko kuma Volodymyr I Sviatoslavych (Sunan Kiristanci: Basil; c. 958 – 15 July 1015), wanda aka ba inkiya da "the Great", ya kasance yariman Novgorod a alif 970 da kuma Babban Yariman Kiev daga 978 har zuwa mutuwar sa a alif 1015. Babban cocin Eastern Orthodox Church sun masa lakabi da Saint Vladimir.
Mahaifin Vladimir shi ne Sviatoslav I na Daular Rurik. Bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 972, Vladimir, wanda a lokacin shi ne yarima na Novgorod, an tilasta masa ya gudu zuwa kasashen waje bayan ɗan'uwansa Yaropolk ya kashe ɗayan ɗan'uwansa Oleg a shekarar alif 977 don ya zama mai mulkin Rus. Vladimir ya tara sojojin Varangian kuma ya dawo don kawar da Yaropolk a cikin shekarar alif 978. Ya zuwa shekara ta 980, [1] Vladimir ya karfafa mulkinsa zuwa Tekun Baltic kuma ya karfafa iyakoki game da hare-hare ga Bulgariyawa, Ƙabilun Baltic da makiyaya na Gabas. [1][2] Asali ya kasance mai bin addinin gargajiya [3][4] na Slavic, Vladimir ya tuba zuwa Kiristanci a cikin 988,[5][6][7] kuma ya kirista Kievan Rus.
Sunan
[gyara sashe | gyara masomin]Masana da yawa suna kiran Vladimir da suna Volodimer, kuma an rubuta Volodimir, da zuriyarsa a matsayin Volodimerovichi (wani lokacin a matsayin "Rurikids").[8][9][10][11][12][10] A Tarihin Scandinavia, an kuma san Vladimir da Valdemar ko Tsohon Norse Valdamarr (duba Waldemar).
Samun iko
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a shekara ta 958, Vladimir shi ne ɗan ƙarami a cikin 'ya'yan Sviatoslav I na Kiev da mai kula da gidansa Malusha.[13] An bayyana Malusha a cikin labaran Norse sagas a matsayin annabiya wacce ta rayu har tsawon shekaru 100 kuma an kawo ta daga kogonta zuwa fada don ta ayyana gaibu. Ɗan'uwan Malusha Dobrynya shine malamin Vladimir kuma amintaccen mai ba da shawara. Hagiographic al'adar shakku ta kuma haɗa ƙuruciyarsa da sunan kakarsa, Olga ta Kiev, wanda Kirista ne kuma ya mallaki babban birnin a lokacin yakin basasa na Sviatoslav.[14]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ National geographic, Vol.
- ↑ Ukrainian Catholic Church: part 1.
- ↑ Saint Vladimir the Baptizer: Wetting cultural appetites for the Gospel, Dr. Alexander Roman, Ukrainian Orthodoxy website
- ↑ Vladimir the Great, Encyclopedia of Ukraine
- ↑ Vladimir the Great, Encyclopedia of Ukraine
- ↑ Saint Vladimir the Baptizer: Wetting cultural appetites for the Gospel, Dr. Alexander Roman, Ukrainian Orthodoxy website
- ↑ Ukrainian Catholic Church: part 1., The Free Library
- ↑ Franklin 1991.
- ↑ Ostrowski 2006.
- ↑ 10.0 10.1 Halperin 2022.
- ↑ Ostrowski 2018.
- ↑ Raffensperger 2016.
- ↑ Bain 1911.
- ↑ Kovalenko, Volodymyr. "Young years of Volodymyr Svyatoslavych: the path to the Kyiv throne in the light of the theories of A. Adler - E. Erikson". Bulletin of the Chernihiv National Pedagogical University. Series: Historical Sciences. 2015 (134): 10–18.