Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Group half.svgMajalisar Ɗinkin Duniya
Flag of the United Nations.svg
Bayanai
Suna a hukumance
United Nations, 联合国, Organización de las Naciones Unidas, Организация Объединённых Наций, منظمة الأمم المتحدة, Organisation des Nations unies, Vereinte Nationen da Organizacja Narodów Zjednoczonych
Gajeren suna UNO
Iri intergovernmental organization (en) Fassara da international organization (en) Fassara
Ƙasa worldwide (en) Fassara
Aiki
Bangare na United Nations System (en) Fassara
Ƙaramar kamfani na
Mulki
Shugaba United Nations Secretary-General (en) Fassara
General secretary (en) Fassara António Guterres
Mamba na board
Hedkwata New York
Subdivisions
Tsari a hukumance intergovernmental organization (en) Fassara
United Nations (Member States and Territories).svg
Tarihi
Ƙirƙira 1945
Wanda ya samar
Wanda yake bi League of Nations (en) Fassara
Awards received

un.org


Facebook icon 192.pngTwitter Logo.pngYoutube-variation.pngInstagram logo 2016.svg

Majalisar Ɗinkin Duniya dai tsari ne wanda kasashen duniya suka amince da kerawa domin magance rikice-rikice da yake faruwa bayan yakin duniya na Biyu (2). An kafa ta ne a shekara ta 1945 domin samar da kwanciyar hakkali a cikin duniya baki daya. Kuma ta kunshi kusan dukkanin kasashen duniya, banda kasashe biyu; palestinu da Saint-siege. Muhimmin Jawabin da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana game da Hakkokin 'Yan-adam a shekara ta 1948.

Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya[gyara sashe | gyara masomin]

Koda yake kafin kafuwar Majalisar ta Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi da aka kafa domin haɗin kai da cigaban ƙasashen duniya, irin su ƙungiyar ma'aikatan sadarwa ta ƙasa da ƙasa a shekara ta 1865 da kuma ƙungiyar ma'aikatan gidajen wasiƙu a shekara ta 1874. Wa'yanda daga bisani suka rikiɗe zuwa hukumomin Majalisar ta Ɗinkin Duniya bayan da aka kafa ta.

Taron farko da aka gudanar a ƙarƙashin lemar Majalisar Ɗinkin Duniya itace wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shine yakai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a ƙasar Holland a shekara ta 1902.

A shekara ta 1945 ne ƙasashen duniya 50 suka gudanar da taro a Jihar San Francisco na Amurika domin ƙaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun haɗa da Amirka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa, wa'yannan ƙasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu ƙarfin faɗa aji.

A ranar 24 ga watan Oktoban shekara ta 1945 ne dai wa'yannan ƙasashe suka rattaba hannu a daftarin ƙarshe da ya kafa Majalisar ta Ɗinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar 24 ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta. Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru 64 da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwan ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma maici yanzu Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu. [1]

Tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya
  Membobin Majalisar Dinkin Duniya
  Jahohin Masu Sa ido na Majalisar Dinkin Duniya (Palestine, Vatican)
  Ƙasashen da ba mamba ba (Niue, Cook Islands)
  Ƙasashen Masu Mulkin Kai
  Antarctica (yankin duniya)
Majalisar Ɗinkin Duniya

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]