Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Majalisar Ɗinkin Duniya
intergovernmental organization, international organization, subject of international law
bangare naUnited Nations System Gyara
farawa1945 Gyara
office held by head of the organizationUnited Nations Secretary-General, general secretary Gyara
secretary generalAntónio Guterres Gyara
board memberKofi Annan Gyara
diplomatic relationTarayyar Turai Gyara
award receivedNobel Peace Prize, Peabody Award, Sakharov Prize Gyara
wanda yake biLeague of Nations Gyara
wurin hedkwatarHeadquarters of the United Nations Gyara
foundational textCharter of the United Nations Gyara
phone number+1-212-963-4475 Gyara
official websitehttps://www.un.org/ Gyara
tutaflag of the United Nations Gyara
tarihin maudu'ihistory of the United Nations Gyara
Unicode character🇺🇳 Gyara
has works in the collectionNational Museum of World Cultures Gyara
maintained by WikiProjectWikiProject United Nations Gyara
Tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya
Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya dai tsari ne wanda kasashen duniya suka amince da kerawa domin magance rikice rikice da yake yake bayan yakin duniya na Biyu (2). An kafa ta ne a 1945 domin sayya kwaciyar hakkali a cikin duniya baki daya. Kuma ta kumshi kusan dukannin kasashen duniya, banda kasashe biyu; palestinu da Saint-siege.Muhimmin Jawabin da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948.

Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya[gyara sashe | Gyara masomin]

Koda yake kafin kafuwan Majalisar ta Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi da aka kafa domin haɗin kai da cigaban ƙasashen na duniya, irin su ƙungiyar ma'aikatan sadarwa ta ƙasa da ƙasa a 1865 da kuma ƙungiyar ma'aikatan gidajen wasiƙu a 1874. Wa'yanda daga bisani suka rikiɗe zuwa hukumomin Majalisar ta Ɗinkin Duniya bayan da aka kafa ta.

Taron farko da aka gudanar a ƙarƙashin lemar Majalisar Ɗinkin Duniya itace wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shine yakai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a ƙasar Holland a 1902.

A 1945 ne ƙasashen duniya 50 suka gudanar da taro a Jihar San Francisco na Amurika domin ƙaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun haɗa da Amirka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa, wa'yannan ƙasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu ƙarfin faɗa aji.

A ranar 24 ga watan Oktoban 1945 ne dai wa'yannan ƙasashe suka rattaba hannu a daftarin ƙarshe da ya kafa Majalisar ta Ɗinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar 24 ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta. Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru 64 da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwan ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma maici yanzu Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu. [1]

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. http://www.dw-world.de/dw/article/0,,5096509,00.html&lt