Makkah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
makkah
Masallaci mai Alfarma na garin Makkah.

Birnin Makkah wani babban gari ne mai tarihi, birnin ya kasance a nahiyar Asiya wato acikin tsibirin Saudiya a tarayyar Larabawa. Wannan gari na Makkah shine birni mafi girma da shahara a duk fadin nahiyar Asiya birni ne wanda Allah yayi masa albarka tunda shine birnin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w). Albarkatun kasa Garin makkah Allah ya azurtashi da yawan bishiyoyin irin su Dabino da Inabi lallai birnin kayataccen birni ne wanda har ya wuci a iya misaltawa, hakazalika ta bangaren albarkatun kasa, Allah ya horewa birnin arzikin man fetur da kuma gwala-gwalai da sauransu.

palm
Irin bishiyoyin dabinon dake Birnin Makkah a kasar Saudi Arabia

Birnin Makkah shine birnin manzon Allah na farko, a garin aka haifeshi a nan kuma yayi girma tun gabanin a bashi Annabta {pp} daga baya ne ya koma Madinah.