Jump to content

Malik Mazhar Abbas Raan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Malik Mazhar Abbas Raan
Member of the Provincial Assembly of the Punjab (en) Fassara

15 ga Augusta, 2018 - 16 ga Janairu, 2019
District: PP-218 Multan-VIII (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Multan (en) Fassara, 1 ga Faburairu, 1953
Mutuwa 16 ga Janairu, 2019
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara
Beautiful view of Punjab Assembly Lahore - panoramio.jpg
Punjab Majalisar Lahore

Malik Mazhar Abbas Raan (An haife shi 1 ga watan Fabrairu shekarar 1953 - Ya rasu 16 ga watan Janairu, shekarar 2019) ɗan siyasan kasar Pakistan ne wanda ya kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab daga shekarar 1997 zuwa shekarar 1999, daga watan Mayu shekarar 2013, zuwa watan Mayu shekarar 2018 da kuma daga watan Yuli shekarar 2018 zuwa watan Janairu, shekarar 2019.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 1953 a Multan . [1]

Ya sauke karatu daga Kwalejin Emerson ta Gwamnati a 1978 kuma yana da digiri na Bachelor of Arts . [1]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya tsaya takarar kujerar majalisar lardin Punjab a matsayin dan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP) daga mazaɓar PP-166 (Multan-VII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 1988, amma bai yi nasara ba. Ya samu kuri'u 21,059 sannan ya sha kaye a hannun Shah Mehmood Qureshi . [2]

Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Lardin Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Democratic Alliance (PDA) daga mazaɓar PP-166 (Multan-VII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 1990, amma bai yi nasara ba. Ya samu kuri'u 22,719 sannan ya sha kaye a hannun Shah Mehmood Qureshi. [2]

An Zaɓe shi a Majalisar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-N) daga mazaɓar PP-166 (Multan-VII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 1997 . Ya samu kuri'u 22,193 sannan ya doke Sajjad Hussain Qureshi . [2]

Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Lardin Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga mazabar PP-201 (Multan-VIII) a babban Zaɓen Pakistan a shekarar 2002, amma bai yi nasara ba. Ya samu kuri’u 25,005 sannan ya sha kaye a hannun Malik Muhammad Arshad Ran Ɗan takarar jam’iyyar PPP

Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Lardin Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-Q) daga mazabar PP-201 (Multan-VIII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 2008, amma bai yi nasara ba. Ya samu kuri'u 25,412 sannan ya sha kaye a hannun Malik Muhammad Abbas Raan Ɗan takarar jam'iyyar PPP. [3]

An sake zaɓen shi a Majalisar Lardin Punjab a matsayin dan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-201 (Multan-VIII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 2013 . Ya samu kuri'u 35,233 sannan ya doke Makhdoom Mureed Hussain Qureshi Ɗan takarar jam'iyyar PPP. [4]

An sake zaɓen shi zuwa Majalisar Lardi na Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) daga mazabar PP-218 (Multan-VIII) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .

Ya mutu a ranar 16 ga watan Janairu, shekarar 2019 dalilin bugun zuciya a Lahore.

  1. 1 2 "Punjab Assembly". www.pap.gov.pk. Archived from the original on 19 June 2017. Retrieved 15 January 2018. Cite error: Invalid <ref> tag; name "pap" defined multiple times with different content
  2. 1 2 3 "Punjab Assembly election result 1988-1997" (PDF). ECP. Archived (PDF) from the original on 30 August 2017. Retrieved 25 March 2018. Cite error: Invalid <ref> tag; name "ecp/1988-97" defined multiple times with different content
  3. "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 24 March 2018.
  4. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 May 2018. Retrieved 12 July 2018.