Man kade

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
mata a Afirka sun kasa man kaɗe suna sayarwa
man kaɗe
barzajjiyar ƙwara kafin a kaishi niƙa an shanya ta a rana
wata Mata tana daddaƙa ƙwara don yin mankaɗe
mata sun ɗauko ƙwara a baho
wajen da akeyin man kaɗe a Ghana

Man kade wani mai ne da ya samo asali daga yayan bishiyar kadanya. Wanda idan aka shanye ya-yan kaden bayan sun nuna to sai a tara ya-yan kaden (qwara), bayan ta taru sai ayi amfani da ita.[1]

Yadda ake yin man kade[gyara sashe | Gyara masomin]

wata tsohuwa tana yin man kaɗe
ƙwarar bishiyar kaɗanya dafaffiya kafin a ƙarasa gyara ta don man kaɗe
dafaffiyar ƙwara kafin a kwalɗeta. Bayan an kwalɗeta sai a shanya ta har ta bushe, sannan a kaita niƙa gurin masu injin
mata na baza ƙwara don shanya ta a rana

Bayan an gama tara qwara, sai a dafa ta sosai bayan an dafa ta sai a sauke ta idan ta huce sai a barta bayan wani dan lokacin kaman sati daya haka tana rana a waje, ko da ana ruwan sama baza ya mata komai ba. Wasu ma suna aje ta bayan an dafa ta tsawon watanni idan bada gaggawa ake sonta ba. Bayan ta sha iska ta saki sai a farfasa a cire bawon mai karfi, Nan ma za'a sake shanya ta a rana nan kam baza a bari ruwa ya jika ta ba. Bayan ta bushe sosai! Sai a barza ta ko a turmi ko a dutse, bayan an gama barza ta sai a kai Nika gurin masu inji na nikan qwara, bayan an niko an dawo ita gida daga nan sai asa ruwa bakin gwargwado man kade yana tasowa ana yade shi. Bayan an gama yade shi a danyen shi sai Kuma a sake soya shi ko kuma narka shi ta yadda zai yi daidai. Daga nan kam sai amfani da shi.

wasu Mata a Afirka suna yin man kaɗe a baho

Amfani shi[gyara sashe | Gyara masomin]

Man kade yana da amfani sosai musamman a jikin Dan Adam ana shafa Shi fata ana kuma shanshi musamman a abinci, amfani Man Kade baya kirguwa yana da matukar amfani

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Mubarak Bala, Muhammad (12 October 2017). "Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia". legit hausa. Retrieved 1 August 2021.