Jump to content

Manufar Biza na Mozambique

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Manufar Biza na Mozambique
visa policy (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Mozambik
Intended public (en) Fassara rest of the world (en) Fassara
Hannun riga da visa requirements for Mozambican citizens (en) Fassara

Mozambique tana ba da damar mafi yawan ƙasashen da ba a keɓe biza su sami biza idan sun isa. Duk da haka, dole ne 'yan ƙasa na wasu ƙasashe su sami takardar visa ta kan layi ko daga ɗaya daga cikin ofisoshin diflomasiyyar Mozambique a duniya kafin a ba su izinin shiga cikin ƙasar.[1]

Mozambik wani bangare ne na kungiyar raya kasashen kudancin Afirka, ma'ana mambobin sauran kasashen SADC ba sa bukatar bizar yawon bude ido idan sun ziyarci Mozambique domin yawon bude ido.

Ƴan ƙasa na waɗannan ƙasashe basa buƙatar biza don shiga Mozambique don tsayawa har tsawon lokacin da aka jera a ƙasa:[2][3]

Isowar Biza

[gyara sashe | gyara masomin]

Jama'ar duk sauran ƙasashen da ba a keɓe biza ba za su iya samun biza idan sun isa Mozambique, mai aiki na tsawon kwanaki 30 a duk wuraren da ke kan iyaka, idan sun gabatar da fasfo mai aiki na tsawon watanni 6 da isowa[4] da dawowa ko tikitin zuwa gaba, da kuma shaidar isassun kudade don tallafawa zamansu da kuma hujjar manufar ziyarar tasu[5]. Bizar da aka samu lokacin isowa tana kashe dalar Amurka 50.

Duk da takardar bizar da ke nuna cewa tana aiki ne don shigarwa 1 kawai, baƙi da suka yi tafiya zuwa Eswatini da Afirka ta Kudu sun gano cewa yana aiki don shigarwa 2 idan har yanzu bizar tana cikin kwanakin 30 ɗin ta.[6]

A cikin Disamba 2022, tsarin e-Biza isa na Mozambique ya fara aiki. 'Yan ƙasa na duk ƙasashen da ba su da izinin biza kuma za su iya neman e-Biza kafin su shiga Mozambique.[7]

  1. Mozambique Government Announces 30-day Tourist Visas now Available at Borders for all Visitors - Mozambican Hotels". www.mozambicanhotels.com. Retrieved 6 December 2017
  2. "Visa Waiver Countries"
  3. Visa and passport". Timatic. International Air Transport Association through Emirates. Retrieved 1 April 2017.
  4. Mozambique Tourism e Visa". www.toursmaputo.com. Retrieved 25 October 2019
  5. Visa and passport". Timatic. International Air Transport Association through Emirates. Retrieved 1 April 2017.
  6. "Mozambique Tourist Visa Now Valid for 2 Entries - Mozambican Hotels". www.mozambicanhotels.com. Retrieved 20 March 2018.
  7. Mozambique Tourism e Visa". www.toursmaputo.com. Retrieved 25 October 2019