Jump to content

Marcello Palmisano

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marcello Palmisano
Rayuwa
Haihuwa San Michele Salentino (en) Fassara, 17 ga Janairu, 1940
ƙasa Italiya
Somaliya
Kingdom of Italy (en) Fassara
Mutuwa Mogadishu, 9 ga Faburairu, 1995
Karatu
Harsuna Italiyanci
Sana'a
Sana'a ɗan jarida
Kyaututtuka
Imani
Addini Kiristanci

Marcello Palmisano (San Michele Salentino, 17 ga Janairun 1940 - Mogadishu, 9 ga Fabrairu, 1995) ɗan jaridar kasar Italiya ne kuma mai ba da rahoto.

Bayan gama makarantar sakandare, Palmisano ya yi hijira zuwa Switzerland, inda ya sami aiki a matsayi a matsayin ma'aikaci. Daga Switzerland ya koma Cologne, a kasar Jamus, inda ya kammala karatu a matsayin mai daukar hoto.

Daga nan sai ya zabi wannan sabon aiki na mai watsa shirye-shiryen jama'a na Switzerland. Komawa Italiya a shekara ta 1972, ya fara aiki ma RAI, mai watsa shirye-shiryen jama'a na Italiya, yana samun ayyuka daban-daban a cikin yanayin yaƙi kamar Kambodiya, Vietnam, Afghanistan, Libya da Somaliya.

Ya mutu a Mogadishu [1] Fabrairu 9, a shekarar 1995, 'yan bindiga na Somaliya suka kashe shi yayin da yake daukan fim game da janyewar Sojojin Amurka. [2][3] Anyi kuskuren shi da wani, yayin da yake bayar da rahoto tare da abokin aiki, Carmen Lasorella wanda ya tsira, yayin janyewar sojojin Amurka. An kama shi a lokacin "banana war" na ƙasar don kula da masana'antar banana, wanda ya haifar da rikice-rikice tsakanin shugabannin yaƙi masu adawa. [4][5]

  1. "36 Journalists Killed in Somalia since 1992 – 2012 | Markacadey.net". www.markacadey.net. Archived from the original on 2012-08-10.
  2. "Kate Peyton - Journalists Killed". Committee to Protect Journalists. 2005-02-09. Retrieved 2012-10-19.
  3. "Marcello Palmisano".
  4. "SOMALIA : BANANA WAR CONTINUES - 25/02/1995 - the Indian Ocean Newsletter". 25 February 1995.
  5. "Marcello Palmisano - The Journalists' Memorial". thejournalistsmemorial.rsf.org. Archived from the original on 2016-03-04.