Maria Kiwanuka
27 Mayu 2011 - 1 ga Maris, 2015 ← Syda Bbumba - Matia Kasaija (en) | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Kampala, 12 Mayu 1955 (70 shekaru) | ||
| ƙasa | Uganda | ||
| Mazauni |
Kololo (en) | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
London School of Economics and Political Science (en) London Business School (en) Jami'ar Makerere Makarantar Sakandare ta Gayaza | ||
| Harsuna | Turanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | Mai tattala arziki, ɗan siyasa, ɗan kasuwa, ɗan kasuwa da minista | ||
|
Mahalarcin
| |||
Maria Kiwanuka (an haife ta a ranar ga watan 12 May, 1955) ƴar ƙasar Uganda ce masaniyar tattalin arziki, 'yar kasuwa kuma ƴar siyasa wacce ta yi ministar kuɗi a majalisar ministocin Uganda daga ranar 27 ga watan May 2011 zuwa ranar 1 ga watan Maris 2015. [1] [2] Tun daga shekarar 2015 ta kasance Babbar mai ba da shawara ga shugaban Uganda kan harkokin kuɗi, wanda ke da alhakin Cibiyoyin Bretton Woods. [3]
Bayani na gaba ɗaya
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin naɗa ta a majalisar ministoci, ta kasance manajin darakta na Radio One and its sister station Radio Two da aka fi sani da Akaboozi FM, a Uganda, inda danginta ke da mafi yawan hannun jari. Har ila yau, ta yi aiki a matsayin mamba ba mai zartarwa a kwamitin gudanarwa na Gidauniyar Aga Khan (Gabashin Afirka), Nabagereka Development Trust, Jami'ar Nkumba, Bankin Raya Uganda da Bankin Stanbic Uganda Limited. [4]
Ta yi aiki a hukumar Stanbic Bank Uganda Limited daga shekarun 2009 har zuwa 2011. Bayan ta yi aiki a matsayin shugabar hukumar gudanarwa a bankin United Bank for Africa Uganda Limited na tsawon shekaru, an naɗa Maria a hukumar Standard Chartered Uganda a watan Mayu 2021. [5]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a Kampala, babban birnin Uganda a ranar 12 ga watan Mayu 1955. [6] Maria Kiwanuka ta halarci makarantar sakandare ta Gayaza, babbar makarantar sakandare ta kwana ta 'yan mata, mai tazarar 26 kilometres (16 mi), ta hanya, arewa maso gabashin Kampala, inda ta kammala a shekarar 1973. A cikin shekarar 1974 ta shiga Jami'ar Makerere, babbar jami'ar ilimi mafi girma a Uganda. Ta kammala karatu a shekarar 1977 tare da digiri a fannin Kasuwanci (BCom). Daga baya ta ci gaba da karatu a Makarantar Kasuwancin London da ke Burtaniya, inda ta kammala digirin ta na Master of Business Administration (MBA). [7]
Gogewa a fannin aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Tun daga shekara ta 1980, ta yi aiki fiye da shekaru goma tare da bankin duniya, a matsayin mai sharhi kan tattalin arziki da harkokin kuɗi na yankunan Gabashin Asiya da Kudancin Afirka. Musamman ta shafi ayyuka a Burma, Malawi, Swaziland da Uganda. Bayan ta bar bankin duniya, ta koma ƙasarta ta Uganda ta shiga harkokin kasuwanci na sirri. Tare da membobin danginta, ta kafa kasuwanci a fannonin watsa shirye-shirye, wallafe-wallafe, gidaje da tuntuɓar tattalin arziki. Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkokin kuɗi ga Nabagereka na Buganda tun farkon shekara ta 2000s. [8] A wani sauyi a majalisar ministocin da aka yi a ranar 1 ga watan Maris, 2015 an cire ta daga majalisar ministocin kuma aka naɗa ta babbar mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin kuɗi. [3]
Ta yi aiki tsawon shekaru a matsayin darekta mara zartarwa a bankin Stanbic Uganda Limited, Gidauniyar Agha Khan, Jami'ar Nkumba da Bankin Raya Uganda. [9] Tun bayan barin majalisar ministocin Uganda a shekarar 2015, ta yi aiki a matsayin shugabar hukumar bankin United Bank for Africa Uganda Limited. Tun daga watan Mayu 2022, tana zaune a kan hukumar Standard Chartered Uganda, a matsayin memba mara zartarwa, tun daga watan Mayu 2021. [10] A watan Mayun 2022, an naɗa Maria Kiwanuka shugabar hukumar a Airtel Mobile Commerce Uganda Limited (AMCUL), reshen Airtel Uganda kuma mai samar da Airtel Money Uganda. [11]
Bayanan sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Ta auri Mohan Kiwanuka, manajin darakta na Oscar Industries Limited. A shekara ta 2007, shekaru huɗu kafin a naɗa ta ministar kuɗi, an saka mijinta a matsayin ɗaya daga cikin masu kuɗi a Uganda. [12] [13]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- KCCA
- Majalisar Uganda
- Majalisar ministocin Uganda
- Yuganda Tattalin Arziki
- Mawadatan Uganda
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Buufu, Emma. "Why Uganda ranks highly in tax administration | supplements".[permanent dead link]
- ↑ "Comprehensive List of New Cabinet Appointments And Dropped Ministers". New Vision via Facebook.com. 27 May 2011. Retrieved 1 March 2015.
- ↑ 3.0 3.1 "Full Cabinet List As At 1 March 2015" (PDF). 1 March 2015. Archived from the original (PDF) on 9 July 2017. Retrieved 1 March 2015.
- ↑ London Business School (December 2021). "Maria Kiwanuka MSc14(1981): Senior Advisor To The President of Uganda". London Business School. Archived from the original on 2 December 2021. Retrieved 2 December 2021.
- ↑ Godfrey Ivudria (20 May 2021). "Standard Chartered Appoints Maria Kiwanuka". Business Week Uganda. Archived from the original on May 20, 2021. Retrieved 2 December 2021.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Profile At Uganda Parliament Website". Parliament of Uganda. Archived from the original on 27 May 2016. Retrieved 16 July 2014.
- ↑ Mutenza, W (30 September 2011). "The East Africa's 10 Most Powerful Women". ThePromota.Co.Uk. Retrieved 16 July 2014.
- ↑ Daniel Kalinaki (30 May 2012). "The Life And Mindset of A Finance Minister". Africareview.com. Archived from the original on 22 July 2015. Retrieved 16 July 2014.
- ↑ Uganda Bettors Association (2017). "Inspiring Story Of Maria Kiwanuka, How She Built Her Multi-Billion Empire". UgandaBettorsAssociation.com. Archived from the original on 16 October 2022. Retrieved 8 April 2022.
- ↑ Godfrey Ivudria (20 May 2021). "Standard Chartered Appoints Maria Kiwanuka". East African Business Week. Archived from the original on May 20, 2021. Retrieved 8 May 2022.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ Javira Ssebwami (5 May 2022). "Former Finance Minister, Maria Kiwanuka named board chair of Airtel Mobile Commerce". PML Daily. Retrieved 8 May 2022.
- ↑ Michael Kanaabi, and Ssebidde Kiryowa (2008). "The Deepest Pockets". New Vision Mobile. Archived from the original on 21 October 2014. Retrieved 16 July 2014.
- ↑ Akumu, Patience (1 January 2013). "Celebrating The Men Behind Successful Women". The Observer (Uganda). Retrieved 16 July 2014.