Marie Van Brittan Brown
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa |
Queens (mul) ![]() |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Ƙabila | Afirkawan Amurka |
Mutuwa |
Jamaica (en) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a |
inventor (en) ![]() |

Marie Van Brittan Brown (Oktoba 30, 1922 - Fabrairu 2, 1999) ma'aikaciyar jinya ce Ba'amurkiya, mijinta Albert L. Brown, ƙwararren masani ne na lantarki. A cikin 1966 sun ƙirƙira tsarin tsaro na gida mai ji da gani[1][2] A wannan shekarar sun nemi takardar izinin tsarin tsaron su. An ba da ita bayan shekaru uku a cikin 1969.[1]
Ahali
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi mahaifin Marie Van Brittan Brown a Massachusetts kuma mahaifiyarta 'yar Pennsylvania ce. Dukansu ’yan Afirka ne. An haifi Marie a Jamaica, Queens, New York.[3]
Marie ta auri Albert L. Brown, shi ma Ba-Amurke. Ma'auratan sun rayu a 151-158 & 135th Avenue a Jamaica, Queens, New York. Ba ta da ‘yan’uwa.[4] Marie da Albert suna da yara biyu. Haka nan ‘yarsu ta zama ma’aikaciyar jinya kuma mai ƙirƙira.[5]
Marie ta mutu a Queens a ranar Fabrairu 2, 1999 tana da shekaru saba'in da shida.[6]
Tsarin tsaro na gida
[gyara sashe | gyara masomin]Adadin laifuka a unguwarsu ya yi yawa sosai kuma 'yan sanda sukan dauki lokaci mai tsawo kafin su iso. Wannan ya sa Browns suka ƙirƙira tsarin tsaro na sauti da bidiyo na gida.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 U.S. patent 3,482,037
- ↑ Baderinwa, Sade (2021-02-23). "Marie Van Brittan Brown of Queens invented the home security system". ABC7 New York. Archived from the original on 2021-02-23. Retrieved 2021-03-08.
- ↑ Inventor Marie Van Brittan Brown born | African American Registry". www.aaregistry.org. Archived from the original on 2016-03-01. Retrieved 2016-02-22.
- ↑ Home security system utilizing television surveillance, 1966-08-01, archived from the original on 2019-02-25, retrieved 2018-04-11
- ↑ Brown, Marie Van Brittan (1922–1999) | The Black Past: Remembered and Reclaimed". www.blackpast.org. 11 April 2016. Archived from the original on 2018-04-18. Retrieved 2018-04-11.[better source needed]
- ↑ Buck, Stephanie (2017-06-13). "This African American woman invented your home security system". Timeline. Archived from the original on 2020-06-10. Retrieved 2019-03-17.
- ↑ "Inventor Marie Van Brittan Brown born | African American Registry". www.aaregistry.org. Archived from the original on 2016-03-01. Retrieved 2016-02-22