Jump to content

Marina Pachinuapa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marina Pachinuapa
Member of the National Defence and Security Council of Mozambique (en) Fassara

26 ga Maris, 2020 -
Rayuwa
ƙasa Mozambik
Sana'a
Sana'a soja, ɗan siyasa da independence fighter (en) Fassara

Marina Pachinuapa 'yar gwagwarmaya yaƙin neman 'yancin kai ce kuma 'yar siyasa ta Mozambique. A shekarar 1977 ta kasance ɗaya daga cikin ruƙunin mata na farko da aka zaɓa a Majalisar Jama'a.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Pachinuapa ta shiga cikin yakin 'yancin kai na Mozambique, wacce ta kafa Ƙungiyar Mata na FRELIMO.[1] Daga baya ta riƙe muƙamin kanar a ajiyar soja,[2] kuma tana cikin waɗanda suka kafa kungiyar mata ta Mozambique.[3] Bayan samun 'yancin kai, ta kasance 'yar takarar FRELIMO a zaɓen 'yan majalisa na 1977,[4] a cikinsa tana ɗaya daga cikin ruƙuni na farko na mata 27 da aka zaɓa a Majalisar Jama'a.[5] An sake zaɓen ta a shekara ta 1986 daga lardin Sofala mai wakiltar masana'antar Moçambique.[6] A shekarar 2010 aka naɗa ta a Majalisar Tsaro da Tsaro ta ƙasa.[7]

  1. MARINA PACHINUAPA ÀS MULHERES: Violência não tem a ver com emancipação Noticias Online, 6 April 2017
  2. Jonna Katto (2014) "Landscapes of Belonging: Female ExCombatants Remembering the Liberation Struggle in Urban Maputo" Journal of Southern African Studies, volume 40, number 3, pp539–557
  3. AIM Reports, issues 332–415, p1
  4. Translations on Sub-Saharan Africa issues 1857–1867, p43
  5. Mart Martin (2000) The Almanac of Women and Minorities in World Politics, p267
  6. 4.° Suplemento Boletim da República, 22 September 1987
  7. 4.° Suplemento Boletim da República, 22 September 1987