Marry my husband
| Marry my husband | |
|---|---|
| Asali | |
| Asalin suna | 내 남편과 결혼해줘, Marry My Husband da Heirate meinen Mann |
| Asalin harshe | Bakoriye |
| Ƙasar asali | Koriya ta Kudu |
| Yanayi | 1 |
| Episodes | 16 |
| Distribution format (en) |
talabijin da video on demand (en) |
| Characteristics | |
| Genre (en) |
revenge series (en) |
| During | 60 Dakika |
| Description | |
| Bisa |
Marry My Husband (en) |
| Ɓangaren |
TvN Monday-Tuesday drama (en) |
| 'yan wasa | |
| Samar | |
| Production company (en) |
DK E&M (en) |
| Screening | |
| Asali mai watsa shirye-shirye |
tvN (en) |
| Lokacin farawa | Janairu 1, 2024 |
| Lokacin gamawa | Fabrairu 20, 2024 |
| External links | |
| tvn.cjenm.com… | |
|
Specialized websites
| |
Marry my husband (Yaren Koriya: 내 남편과 결혼해줘) shirin talabijin ne mai dogon zango na Koriya ta Kudu na shekarar 2024 wanda Shin Yoo-dam ya rubuta, kuma ya ƙunshi jarumai Park Min-Young, Na In-woo, Lee Yi-kyung, da Song Ha-yoon. An shirya shi ne bisa tsarin littafin labari na yanar gizo mai suna iri ɗaya dashi, wanda kuma aka jera shi azaman shafin yanar gizo.[1] An fitar dashi a TVN daga Janairu 1, 2024 zuwa Fabrairu 20, 2024, kowace Litinin da Talata a 20:50 (KST).[2] Hakanan ana samunsa aTVING a Koriya ta Kudu, da kan Amazon Pria cikin zaɓaɓɓun yankuna na duniya ban da Koriya ta Kudu da China.[3][4]
Abubuwan da suka faru
[gyara sashe | gyara masomin]shirin ya fara da abubuwan da suka faru a ranar 12 ga Afrilun shekarar 2023, inda Kang Ji-won ke fama da cutar kansa ta ciki. Bayan kama mijinta, Park Min-hwan, a kan gado tare da babban kawarta, Jeong Su-min, rikici ya faru inda Min-hwan ya kashe Ji-won a bisa kuskure. Ji-won daga nan sai kwatsam ta tsinci kanta a wurin aikinta a cikin shekara ta 2013, bayan an dawo da ita cikin lokacin baya bayan tsoma bakin ruhin mahaifinta. Yayin da take raya rayuwarta da ilimi da bayanai iri ɗaya kamar yadda aka yi a cikin jerin lokutan baya, ta gano cewa don yin rayuwa mai kyau, dole ne ta miƙa rashin sa'ar ta ga wasu. Daga nan ta yanke shawarar Su-min ta auri Min-hwan domin ta rama da kuma kubuta daga mummunar makomarta.
Yayin da shirin ke ci gaba, ta gano cewa manajanta, Yoo Ji-hyuk, shi ma an mayar da shi cikin lokacin baya bayan mutuwarsa a wani hatsarin mota. Ji-hyuk, wanda ya san cewa Min-hwan yana bayan mutuwar Ji-won, kuma ya ƙaunaci Ji-won a cikin jerin lokaci na baya, ya yanke shawarar kare Ji-won a kowane farashi. Bayan Su-min ta auri Min-hwan, Ji-won ta fara dangantaka da Ji-hyuk, amma tsohuwar budurwarsa Oh Yu-ra ta shiga tsakani.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Shin, Eun-joo (February 8, 2023). '전남친 구속' 박민영, 컴백 임박..."'내 남편과 결혼해줘' 검토 중" [공식] ['Ex-boyfriend arrested' Park Min-young, comeback imminent..."'Marry My Husband' under review" [Official]] (in Korean). TV Report. Archived from the original on October 25, 2023. Retrieved October 25, 2023 – via Naver.
- ↑ Moon, Ji-yeon (October 25, 2023). [공식] 박민영·나인우, '내 남편과 결혼해줘' 회귀 로맨스 호흡 [[Official] Park Min-young and Na In-woo, a return romance in 'Marry My Husband'] (in Korean). Sports Chosun. Archived from the original on October 25, 2023. Retrieved October 25, 2023 – via Naver.
- ↑ Hicap, Jonathan (December 11, 2023). "Korean revenge drama 'Marry My Husband' to stream exclusively on Prime Video". Manila Bulletin. Archived from the original on December 11, 2023. Retrieved December 11, 2023.
- ↑ Jin, Byung-hoon (January 1, 2024). 내 남편과 결혼해줘' 인물관계도 및 몇부작? [Marry My Husband' Character Chart and How Many Episodes?]. NBNTV (in Korean). Archived from the original on January 3, 2024. Retrieved January 3, 2024.