Jump to content

Martin Luther King Jr.

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Martin Luther King Jr.
Lua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'.
Murya
Rayuwa
Cikakken sunaMichael King Jr.
HaihuwaAtlanta, 15 ga Janairu, 1929
ƙasaTarayyar Amurka
ƘabilaAfirkawan Amurka
MutuwaSt. Joseph's Hospital (en) Fassara da Memphis, 4 ga Afirilu, 1968
MakwanciMartin Luther King Jr. National Historical Park (en) Fassara
Yanayin mutuwakisan kai (gunshot wound (en) Fassara)
Killed byJames Earl Ray (mul) Fassara
Ƴan uwa
MahaifiMartin Luther King Sr.
MahaifiyaAlberta Williams King
Abokiyar zamaCoretta Scott King (mul) Fassara  (18 ga Yuni, 1953 -  4 ga Afirilu, 1968)
Yara
AhaliChristine King Farris (en) Fassara da A. D. King (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
MakarantaCandler School of Theology (en) Fassara
Boston University School of Theology (en) Fassara
David T. Howard High School (en) Fassara
Washington High School (mul) Fassara
Morehouse College (en) Fassara
(1944 - 1948) Bachelor of Arts (mul) Fassara : kimiyar al'umma
Crozer Theological Seminary (en) Fassara
(1948 - 1951) Bachelor of Divinity (en) Fassara
Boston University
(1951 - 5 ga Yuni, 1955) Ph.D. (mul) Fassara : systematic theology (en) Fassara
Matakin karatuPh.D. (mul) Fassara
Thesis directorLotan Harold DeWolf (en) Fassara
HarsunaTuranci
Sana'a
Sana'apastor (en) Fassara, mai da'awa, civil rights advocate (en) Fassara, peace activist (en) Fassara, pacifist (en) Fassara, marubuci, ɗan siyasa, dan jarida mai ra'ayin kansa, shugaban addini, Malamin addini da parson (en) Fassara
Tsayi176.5 cm
EmployersDexter Avenue Baptist Church (en) Fassara
Ebenezer Baptist Church (en) Fassara
Vrije Universiteit Amsterdam (mul) Fassara
Kyaututtuka
Ayyanawa daga
Wanda ya ja hankalinsaReinhold Niebuhr (en) Fassara, Howard Thurman (en) Fassara, Walter Rauschenbusch (en) Fassara, Henry David Thoreau (mul) Fassara da Mahatma Gandhi
MambaAmerican Academy of Arts and Sciences (en) Fassara
Southern Christian Leadership Conference (en) Fassara
Alpha Phi Alpha (en) Fassara
Progressive National Baptist Convention (en) Fassara
Fafutukacivil rights movement (en) Fassara
Rashin tashin hankali
labor movement in the United States (en) Fassara
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam
Feast
Martin Luther King Jr. Day (en) Fassara
Imani
AddiniBaptists (en) Fassara
IMDbnm0455052
thekingcenter.org

Martin Luther King Jr. (15 ga watan Janairu, 1929 - 4 ga watan Afrilun 1968) ɗan gwagwarmaya ne na kare haƙƙin bil'adama daga ƙasar Amurka. Ya kasance limamin cocin Baftis kuma babban jagora a fafutukar kawar da wariyar launin fata a Amurka ta hanyar amfani da dabarun rashin tashin hankali da sulhu.[1]

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Martin Luther King Jr. a ranar 15 ga watan Janairu, 1929 a garin Atlanta, jihar Georgia dake Amurka. Mahaifinsa, Martin Luther King Sr. limamin coci ne, yayin da mahaifiyarsa Alberta Williams King ta kasance malama. Ya tashi cikin iyali mai kishin addini da ilimi.

King ya halarci Morehouse College, inda ya karanci falsafa. Daga nan ya tafi Crozer Theological Seminary inda ya sami digiri, kafin daga bisani ya kammala karatun digirin digirgir (Ph.D.) a Boston University a shekarar 1955.

Gwagwarmaya

[gyara sashe | gyara masomin]

King ya fara shahara bayan ya jagoranci zanga-zangar a Montgomery, Alabama, don kawo ƙarshen wariyar launin fata a motocin haya. Ya kafa Southern Christian Leadership Conference (SCLC) a shekarar 1957, wanda ya zama wata babbar kungiyar fafutuka. Ya shahara da jawabin “I Have a Dream” da ya gabatar a gaban dubban mutane a Washington DC a 1963.

An kashe Martin Luther King Jr. a ranar 4 ga Afrilu 1968 a otal ɗin Lorraine Motel da ke Memphis, Tennessee, lokacin da yake jagorantar wani gangamin ma'aikatan tsafta. Kisan nasa ya tayar da hankula a faɗin Amurka da ma duniya baki ɗaya.

An karrama Martin Luther King Jr. da Nobel Peace Prize a 1964, sannan kuma aka ƙirƙiri ranar tunawa da shi a matsayin hutun ƙasa a Amurka wato Martin Luther King Jr. Day wanda ake gudanarwa a kowace ranar Litinin ta uku a watan Janairu.

  1. ↑ "Timeline of MLK Assassination and Investigation Into His Killing". Voice of America. Archived from the original on August 2, 2019.