Jump to content

Mary Kay Ash

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mary Kay Ash
Rayuwa
Cikakken suna Mary Kathlyn Wagner
Haihuwa Cypress (en) Fassara, 12 Mayu 1918
ƙasa Tarayyar Amurka
Mutuwa Dallas, 22 Nuwamba, 2001
Makwanci Hillcrest Cemetery (en) Fassara
Ƴan uwa
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta University of Houston (en) Fassara
Heights High School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa
Kyaututtuka

Mary Kay Ash (an haife ta da suna Mary Kathlyn Wagner; 12 ga Mayu, 1918 – 22 ga Nuwamba, 2001) ta kasance ’yar kasuwa ’yar Amurka kuma ta kafa kamfanin tallace-tallacen kayan kwalliya na tsarin rarraba na matakai da dama da ake kira Mary Kay Cosmetics, Inc. A lokacin rasuwarta, tana da dukiya mai darajar dala miliyan 98, kuma kamfaninta yana da fiye da dala biliyan 1.2 na tallace-tallace, tare da masu sayarwa fiye da 800,000 a ƙasashe fiye da talatin da shida.

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mary Kay Ash, wadda aka haifa da suna Mary Kathlyn Wagner a Hot Wells, cikin Harris County, Texas, ita ce 'yar Edward Alexander da Lula Vember Hastings Wagner. Mahaifiyarta ta koyi aikin jinya amma daga baya ta koma shugabar gidan cin abinci a birnin Houston.

Mary Kay ta halarci makarantar Dow Elementary School da kuma Reagan High School a Houston, inda ta kammala karatu a shekarar 1934.

Ta auri Ben Rogers tana da shekara 17. Sun haifi yara uku: Ben Jr., Marylin Reed, da Richard Rogers. A lokacin da mijinta ke aikin soja a Yaƙin Duniya na Biyu, tana saida littattafai ta shiga gida-gida. Bayan mijinta ya dawo daga yaƙi a shekarar 1945, sun rabu da juna (sun sake aure).

Daga bisani, Mary Kay ta sake aure da Charles Weaver, wanda shi ne ɗan'uwan Mary C. Crowley, wadda ta kafa kamfaninkayan cikin gida da kyaututtuka.