Masarautar Kano

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Masarautar Kano
geographical object
ƙasaNijeriya Gyara
coordinate location12°0′0″N 8°31′0″E Gyara
Tutar masarautar Kano da ake amfani da ita a masarautar

Masarautar Kano masarauta ce ta Musulunci datake a birnin Kano na Arewacin Jamhuriyar Najeriya. Fulani ne suke jagorancin masarautar tun a shekarar 1805 lokacin da Muajaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo ya kaddamar da jihadi kan Haɓe wato Hausawa Maguzawa wadanda suka kafa masarautar. Saidai kuma masarautar ta Kano ta rage karfinta tun bayan da turawan mulkin mallaka suka shigo Kasar Arewa.

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Masarautar kano ta fara ne daga wani dan karamin gari dake a zagaye da Dutsen dala a tsakiyar birnin a yanzu. A tabakin masana tarihin sarautar kano sunce "wani jarumi ne mai suna Bagauda ya fara kafa Masarautar tare da zama sarkin ta a shekarar 999. Sai Mihammadu Rumfa wanda yayi kokarin mayarda masarautar maibin tafarkin addinin Musulunci wanda yahau karagar mulki a 1463 zuwa 1499. Masarutar ta Haɓe tacigaba da rike ragamar sarautar ta kano har zuwan jihadin mujaddadi Usaman dan Fodiyo a shekarar 1805.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]