Jump to content

Masha Allah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masha Allah
fixed expression (en) Fassara, Islamic term (en) Fassara da Sufi terminology (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Zikiri
Fuskar Musulunci da Sufiyya
Suna a harshen gida Masya Allah
Tsarin rubutu Arabic script (en) Fassara da Baƙaƙen boko
Soundex (en) Fassara M240
Cologne phonetics (en) Fassara 685
Caverphone (mul) Fassara MSYL11
Mashallah a cikin rubutun Larabci

Mashallah ko Ma Sha Allah ko Masha Allah ko Ma Shaa Allah na(Arabic: مَا شَاءَلََّٰهُ, , lit. "Allah ya so shi' ko 'Kamar yadda Allah ya so") [bayanin 1] kalma ce ta Larabci da aka saba amfani da ita don nuna wani abu mai girma ko kyau da kuma nuna jin tsoro na kyau. Sau da yawa ana amfani da shi don nuna girmamawa da kuma karewa daga mummunar ido, yana nuna cewa mai magana yana yarda da wani abu mai kyau ba tare da yin kishi ba.

Magana ce ta yau da kullun da ake amfani da ita a duk faɗin duniya mai Magana da Larabci da Musulmi, da kuma tsakanin masu magana da Lrabci wadanda ba Musulmai ba, musamman Kiristoci masu magana da Larabci da sauransu waɗanda ke magana da Allah da sunan Larabci Allah.

Ma anar Kalman

[gyara sashe | gyara masomin]



Asalin kalmar shāʾ yana daga tushen haruffa uku na Larabci: shīn (ش), yāʼ (ي), da hamza (ء), wanda ke nufin “so” ko “nufi”. Wannan tushe ana kiransa mai rauni sau biyu (doubly weak root). Fassarar kalmar Mā shāʾ Allāh kai tsaye zuwa Turanci ita ce “Allah Ya so haka” ko “Abin da Allah Ya so ne ya faru”. Kalmar tana nuna cewa abin da ya faru ya kasance ne bisa ga nufin Allah, wanda ke ƙarfafa muhimmin akidar Musulunci ta ƙaddara (kaddarar Allah).

Ma'anar Masha allah a zahiri ita ce "Allah ya nufa", a ma'anar "abin da Allah ya nufa ya faru"; ana amfani da shi wajen cewa wani abu mai kyau ya faru, ana amfani da shi a lokacin da ya gabata. Insha Allah, a zahiri "idan Allah ya nufa", ana amfani da shi makamancin haka amma yana nufin wani abu da zai faru nan gaba.

Ana fada a wajajen kamar haka

[gyara sashe | gyara masomin]

Ana iya amfani da Mashallah don taya wani murna. Tunatarwa ce cewa duk da cewa ana taya mutumin murna, a ƙarshe Allah ya nufa.[ A wasu al'adu, mutane na iya furta Mashallah da imanin cewa zai iya taimakawa wajen kare su daga kishi, mugun ido ko aljani. Kalmar ta kuma shiga cikin harshen magana na harsunan da ba na Larabawa ba waɗanda galibi Musulmai ne, waɗanda suka haɗa da 'yan Indonesia, Malaysia, Farisa, Kashmir, Turkawa, Kurdawa, Bosnia, Azerbaijan, Somaliya, Swahili, Chechens, Avars, Circassians, Bangladeshis, Tatars, Albanians, Uzbeks, Kazakhs, Turkmens, Tajiks, Afghans, Pakistan, da Musulmai Indiya..[1] .[ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (July 2024)">citation needed</span>]

Wasu Kiristoci da sauransu suna amfani da shi a yankunan da Daular Ottoman ke mulki; Serbs, Kiristoci Albaniyawa, Bulgarians, da Macedonians suna cewa ma'a ("mašala"), sau da yawa a ma'anar "aiki da aka yi da kyau", tare da wasu Georgians, Armenians, Bosnian Croats, Pontic Greeks (ya'yan waɗanda suka zo daga yankin Pontus), Greek Cypriots, [2] da Sephardic Yahudawa.[3]

 

Page Samfuri:Reflist/styles.css has no content. 

  1. Empty citation (help)
  2. "μάσιαλλα". Archived from the original on 29 November 2022. Retrieved 10 August 2019.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  3. Naar, Devin E. (2019-01-31). "Sephardic Studies and the boundaries of Jewish Studies: A year in review". jewishstudies.washington.edu.