Jump to content

Mashigar Ruwa ta Bahr Yussef

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mashigar Ruwa ta Bahr Yussef
General information
Height above mean sea level (en) Fassara48 m
Tsawo220 km
Suna bayanAnnabi Yusuf
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa29°14′29″N 30°55′00″E / 29.2415°N 30.9167°E / 29.2415; 30.9167
KasaMisra
TerritoryFaiyum Governorate (en) Fassara
Bahr Yussef kusa da garin Minya

Bahr Yussef (Larabci|بحر يوسف; "hanyar ruwa ta Yusufu"[1]) wani kanal ne da ya hada Kogin Nile da Yankin Dausayi na Faiyum a kasar Misra.

A zamanin duni, Helenawa sun kira shi da Tomis , wanda aka samo shi daga sunansa na Masar Tm.t ("karshen kanal"). Har yanzu ana amfani da wannan sunan bayan fatarar Larabawa a Masar, inda aka fassara shi zuwa Larabci da al-Manhi (Script error: The function "langx" does not exist.).[2] An kuma san shi da "Babban kanal" (Script error: The function "langx" does not exist.) ko "kanal din Moeris".[3] Sunan Larabci na zamani yana komawa ne ga annabi Yusuf, wanda yake shi ne takwaransa a Alkur'ani na Yusufu na cikin Littafi Mai Tsarki.[2]

A zamanin kafin tarihi, kanal din ya kasance madogaran ruwa ce ta dabi'a daga Kogin Nile wacce ta samar da tabki zuwa yamma lokacin da ambaliyar ruwa ta yi yawa. Tun daga Masarautu na Goma sha Biyu, aka fadada hanyar ruwan sannan aka habaka Faiyum domin fadada Lake Moeris (wanda yanzu ake kira Birket Qarun). An gina kanal din ne a cikin gangaren dabi'a na kwarin, wanda ya samar da hanyar ruwa mai tsawon kilomita 15 da zurfin mita 5 wacce ta gangara zuwa cikin ramin Faiyum. Ana sarrafa kanal din ne ta hanyar Dam din Ha-Uar, wanda a zahiri dam guda biyu ne da ke daidaita kwararar ruwa zuwa cikin tabkin da kuma ficewa daga Kogin Nile. Yayin da yankin da ke kewaye ya canza a kusan shekara ta 230 BC, a hankali aka yi watsi da Bahr Yussef, wanda hakan ya sa mafi yawancin Lake Moeris ya kafe, inda ya bar ramin da ke akwai a yau da kuma Yankin Dausayi na Faiyum na zamani.

A lokacin zamanin tsakiya, kanal din ya kasance muhimmiyar hanyar sadarwa domin hada Faiyum da Alkahira.[4]

Har yanzu Bahr Yussef yana nan a yau, inda yake kai ruwa zuwa arewa zuwa cikin Yankin Dausayi na Faiyum, a layi daya da Kogin Nile.

  1. Kalmar Larabci da ke nufin Bahr a zahiri tana nufin "teku", ba "kogi" ba, wanda kuma zai kasance "Nahr").
  2. 1 2 Peust, Carsten (2010). Die Toponyme vorarabischen Ursprungs im modernen Ägypten. Göttingen. p. 103.
  3. "TM Places". www.trismegistos.org. Retrieved 2020-12-06.
  4. Tillier, Mathieu; Vanthieghem, Naïm (July 2020). "Un voyageur témoin de manoeuvres militaires dans le Fayoum (IIIe-IVe/IXe-Xe siècle)" (PDF). Chronique d'Égypte. 95 (190): 347–367. doi:10.1484/J.CDE.5.124771. S2CID 238100373 Check |s2cid= value (help).