Jump to content

Mata Marubutan Zimbabwe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mata Marubutan Zimbabwe
Bayanai
Iri association (en) Fassara
Ƙasa Zimbabwe
Tarihi
Ƙirƙira 1990

Marubuta Mata na Zimbabwe ( ZWW ) kungiya ce ta marubuta mata zalla, da aka kafa a shekarar 1990 a ƙasar Zimbabwe. Ita ce "kungiyar mata ta farko a kasar Zimbabwe haka zalika ta farko a Kudancin Afirka don magance matsalar rashin daidaito tsakanin jinsi ta hanyar rubutu da bugawa ko wallafawa".[1]

An kafa kungiyar don amsa buƙatun da aka bayyana a taron bitar marubuta na 1990, ZWW , har wayau kungiyar na da rassa fiye da casa'in a faɗin ƙasar Zimbabwe a alƙaluma ƙididdigar farkon karni.[2] A cikin shekaru goma na farko daga sadda aka assasa ƙungiyar, ta buga littattafai sama da ɗari biyu na mata, cikin yaruka ko harshen Turanci, Shona da Ndebele.[3] A shekarar 1990 wasu tsirarun marubuta mata ne suka kafa kungiyar ; Marubutan Mata na Zimbabwe (ZWW) don inganta rubuce-rubucen mata a ƙasar. Kawo yanzu, ƙungiyar tana da mambobi 600 da rassa 56 a yankunan karkara da birane a fadin ƙasar.[4]

Wallafe-wallafe

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Kitson, Norma, Anthology of Zimbabwe Women Writers. Zimbabwe: ZWW, 1994. With a foreword by David Karimanzira.
  • Selections: English Poetry and Short Stories. Harare: ZWW, 1997, repr. 2001.
  • Inkondlo [Selections]. Harare: ZWW, 1998. (A Ndebele anthology.)[5]
  • Nhetembo [Selections]. Harare: ZWW, 1990. (A Shona anthology.)
  • Women of Resilience: The voices of women ex-combatants. Harare: Zimbabwe Women Writers, 2000.
  • A Tragedy of Lives. Harare: Zimbabwe Women Writers, 2003.
  1. Tando, Mary O. (2007). "Zimbabwe Women Writers, 1990–2004". In Lydia Alpízar Durán; Noël D. Payne; Anahi Russo (eds.). Building Feminist Movements and Organizations: Global Perspectives. Zed Books. pp. 131–. ISBN 978-1-84277-850-0.
  2. Cheris Kramarae; Dale Spender (2004). Routledge International Encyclopedia of Women: Global Women's Issues and Knowledge. Routledge. p. 1709. ISBN 978-1-135-96315-6.
  3. Kathleen E. Sheldon (2005). "Zimbabwe Women Writers". Historical Dictionary of Women in Sub-Saharan Africa. Scarecrow Press. p. 275. ISBN 978-0-8108-5331-7.
  4. "ZIMBABWE: Women of Zimbabwe tell Their Stories". PeaceWomen (in Turanci). 2015-02-03. Retrieved 2021-11-08.
  5. Zimbabwe Women Writers (1998). Selections Inkondlo. Harare: Zimbabwe Women Writers. pp. 28–30, 37, 48–50.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]