Mgeni Jadi Kadika
29 Oktoba 2015 - Election: 2015 Tanzanian general election (en)
2005 - 2010 | |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | 1957 (68/69 shekaru) | ||||
| ƙasa | Tanzaniya | ||||
| Harshen uwa | Harshen Swahili | ||||
| Karatu | |||||
| Harsuna |
Turanci Harshen Swahili | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Mgeni Jadi Kadika (an haife ta a shekara ta 1957) 'yar majalisar dokokin Tanzaniya ce ta ƙungiyar Civic United Front. [1]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Mgeni Kadika ta yi karatunta a Pandani, Pemba North, ta bar sakandare a shekara ta 1976. Daga shekarun 1977 zuwa 1980 ta yi aiki a ma'aikatar kasuwanci ta Zanzibar, kuma daga shekarun 1980 zuwa 1988 ta kasance manaja a wani shagon haɗin gwiwa.[1]
Ta shiga majalisar dokoki ta ƙasa a shekarar 2005 a matsayin 'yar majalisar wakilai ta musamman ƙarƙashin jam'iyyar Civic United Front, kuma ta riƙe kujerarta a zaɓukan 2010 da 2015.[1]
A watan Mayu 2016, Kadika ta tambayi ko gwamnati za ta ba da ilimin jama'a da bincike kan cutar fibroids na mahaifa.[2] A watan Afrilun shekara ta 2020 ta nuna damuwarta kan ƙaruwar cutar koda a Tanzaniya, kuma ta nemi Ministan Lafiya, Ummy Mwalimu, da ta fitar da kididdigar yankin.[3] A watan Mayun 2020, ta tambayi Ministar Lafiya, Ummy Mwalimu, wane irin matakin da gwamnatin Tanzaniya ke ɗauka, wanda ya wuce tantance iyaka, don kare 'yan ƙasar Tanzaniya daga COVID-19.[4][5]
Mgeni Kadika tana ɗaya daga cikin 'yan majalisa 21 da suka sauya sheka daga CUF zuwa ACT-Wazalendo a watan Yuni 2020.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Hon. Mgeni Jadi Kadika". Parliament of Tanzania. Archived from the original on 24 September 2018. Retrieved 14 February 2021.
- ↑ Felister Peter (5 May 2016). "Plans afoot to permanent community health officers". IPP Media. Retrieved 14 February 2021.
- ↑ "Tanzania: Dar Leads in Kidney Complications, Traced to Modern Lifestyle". Tanzania Daily News. 16 April 2020. Retrieved 14 February 2021.
- ↑ Henry Mwangonde (22 May 2020). "The govt has managed care systems & emerging infections to the country". IPP Media. Retrieved 14 February 2021.
- ↑ "State enhances patients' screenings at grassroots, MPs told". Daily News. 22 May 2020. Archived from the original on 9 June 2020. Retrieved 14 February 2021.
- ↑ "ACT receives 21 defecting MPs". The Citizen. 21 June 2020. Retrieved 14 February 2021.[permanent dead link]