Jump to content

Mir Aamir Ali Khan Magsi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mir Aamir Ali Khan Magsi
Member of the 14th National Assembly of Pakistan (en) Fassara

1 ga Yuni, 2013 -
District: NA-206 (Qambar Shahdadkot) (en) Fassara
Member of the National Assembly of Pakistan (en) Fassara


District: NA-203 Kambar Shahdadkot-II (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 27 Disamba 1960 (65 shekaru)
ƙasa Pakistan
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Pakistan Peoples Party (en) Fassara

Mir Aamir Ali Khan Magsi ( Urdu  ; an haife shi 27 Disamban shekarar 1960) [1] ɗan siyasan Pakistan ne kuma memba na wa'adi uku na Majalisar Dokokin Pakistan (Agusta 2018 har zuwa Agustan shekarar 2023, 2008 zuwa Mayu 2018 kuma tun Fabrairun shekarar 2024).

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓe shi ɗan majalisar dokokin Pakistan a matsayin dan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP) daga mazabar NA-206 (Kamber Shahdadkot) a babban zaɓen Pakistan na 2008 . Ya samu ƙuri'u 49,524 sannan ya doke Nawabzada Sardar Khan Chandio, dan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (Q) (PML-Q). [2]

An sake zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin dan takarar PPP daga Mazabar NA-206 (Kamber Shahdadkot) a babban zaɓen Pakistan na 2013 . Ya samu kuri'u 87,789 sannan ya doke Asgher Shah Rashdi, ɗan takarar jam'iyyar Sindh United Party . A wannan zaɓen, ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Sindh a matsayin dan takara mai zaman kansa daga mazaɓar PS-40 (Larkana-VI) amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 132 sannan ya sha kaye a hannun Mir Nadir Ali Khan Magsi . [3]

An sake zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin dan takarar PPP daga NA-203 (Qambar Shahdadkot-II) a babban zaɓen Pakistan na 2018 .

An sake zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar PPP daga NA-197 Qambar Shahdadkot-II a babban zaɓen Pakistan na 2024 . Ya samu kuri'u 88,130 sannan ya doke Muhammad Uzair Jagirani ɗan takarar jam'iyyar Jami'atu Ulema-e-Islam (JUI(F)) .[4]

  1. "Detail Information". 19 April 2014. Archived from the original on 19 April 2014. Retrieved 11 July 2017.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  2. "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 12 May 2018.
  3. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 12 April 2018.
  4. "Election Commission of Pakistan". ecp.gov.pk. Archived from the original on 2024-01-06. Retrieved 2024-07-17.