Jump to content

Miria Obote

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Miria Obote
First Lady of Uganda (en) Fassara

15 ga Afirilu, 1966 - 25 ga Janairu, 1971
Rayuwa
Haihuwa Kampala, 16 ga Yuli, 1936 (89 shekaru)
ƙasa Uganda
Ƴan uwa
Abokiyar zama Milton Obote
Karatu
Makaranta Jami'ar Makerere
Makarantar Sakandare ta Gayaza
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa Majalisar Jama'ar Uganda
Miria Obote tana jawabi

Miria Obote (née Kalule; an haife ta a ranar 16 ga watan Yuli shekara ta 1936) 'yar siyasar Uganda ce wacce ta kasance uwargidan shugaban ƙasar Uganda, kuma matar tsohon Firayim Minista kuma Shugaba Milton Obote.[1] Ta kasance 'yar takara a babban zaɓen ƙasar Uganda na shekara ta 2006. [2]

Tarihi da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Miria Kalule a Kawempe, ɗiya ce ga Bulasio Kalule, ma'aikacin gwamnati wanda ya yi aiki tare da Sashen Kula da Hanya a Ma'aikatar Ayyuka [3] da matarsa Malita. [4]

Ta halarci makarantar sakandare ta Gayaza daga baya Jami'ar Makerere. [5] [6][7]

Miria Obote ta koma Uganda daga Zambia a watan Oktoba shekara ta 2005, [8] bayan shekaru 20 a gudun hijira, don binne mijinta.[9] Bayan watanni biyu an zaɓe ta a matsayin shugabar jam'iyyar UPC ta Uganda da kuma 'yar takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa. Mijinta [10] ne ya kafa UPC kuma shi ya jagorance shi har mutuwarsa. Ta samu kashi 0.6% na kuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 23 ga watan Fabrairu,shekara ta 2006, wanda shugaba mai ci, Yoweri Museveni ya lashe.[11]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Miria ta auri Milton Obote a watan Nuwamba 1963 [12] [13] kuma suna da 'ya'ya 4, ciki har da Jimmy Akena, ɗan majalisa mai wakiltar Lira Municipality. [14]

Milton Obote ta mutu a ranar 10 ga watan Oktoba shekara ta 2005 a Johannesburg, Afirka ta Kudu, tana da shekaru 79; kuma anyi matajana'iza a ƙasar a birnin Kampala na ƙasar Uganda, wanda ya samu halartar shugaba Yoweri Museveni. [15][16]

  1. "Obote buried in Ugandan home town" (in Turanci). 2005-10-24. Retrieved 2019-06-01.
  2. Dunleavy, Patrick; Diwakar, Rekha (2011-09-11). "Analysing multiparty competition in plurality rule elections" (PDF). Party Politics. 19 (6): 855–886. doi:10.1177/1354068811411026. ISSN 1354-0688. S2CID 18840573.
  3. "Miria shared a life with Obote for 40 years". www.newvision.co.ug. Retrieved 2019-07-11.
  4. @watchdoguganda (2018-11-16). "Miria Kalule Obote fights for life to retain record as the only living former First Lady". Watchdog Uganda (in Turanci). Retrieved 2019-07-11.
  5. "The First Lady who dared to replace her husband". www.newvision.co.ug. Retrieved 2019-07-11.
  6. "Meeting Mama Miria". The Independent Uganda (in Turanci). 2012-07-01. Retrieved 2019-07-11.
  7. Marshall, Julian (11 October 2005). "Milton Obote". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077.
  8. "Miria shared a life with Obote for 40 years". www.newvision.co.ug. Retrieved 2019-06-01.
  9. "Obote buried in Ugandan home town" (in Turanci). 2005-10-24. Retrieved 2019-06-01.
  10. "Like Obote, like son". The Independent Uganda (in Turanci). 2015-07-19. Retrieved 2019-06-01.
  11. "Obote buried in Ugandan home town" (in Turanci). 2005-10-24. Retrieved 2019-06-01.
  12. "UPC ..::|::.. Uganda Peoples Congress". www.upcparty.net. Retrieved 2019-07-11.
  13. "The First Lady who dared to replace her husband". www.newvision.co.ug. Retrieved 2019-07-11.
  14. "Parliament of Uganda". www.parliament.go.ug. Retrieved 2019-07-11.
  15. Nye, Louis (12 October 2005). "Obituaries: Milton Obote of Uganda". The New York Times.
  16. Marshall, Julian (11 October 2005). "Milton Obote". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077.