Jump to content

Mlozi bin Kazbadema

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mlozi bin Kazbadema
Rayuwa
Mutuwa 1895
Sana'a
Sana'a slave trader (en) Fassara

Mlozi bin Kazbadema ko Mlozi kawai (ya mutu a shekara ta 1895) ɗan kasuwan bayi ne na Afirka.[1]

Ya kafa wata babbar daula ta cinikin bayi a Malawi, wacce ya ayyana a matsayin Sultanate, kuma ta zama hanyar jigilar bayi daga cikin Afirka zuwa gabar tekun Swahili na gabashin Afirka da kuma ƙasashen Larabawa ta hanyar cinikin bayi a tekun Indiya. Ya kasance babban jigon yakin Karonga da Birtaniya, kuma an daɗe ana alakanta shi da cinikin bayi na gabashin Afirka.[2]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mlozi ya kasance ɗan kasuwar cinikin bayi na Larabawa na Swaihili daga gabar tekun Swahili.

A cikin shekarar 1879, shi da abokan aikinsa sun kafa cibiyar kasuwanci a yankin ƙabilar Ngonde a cikin kwarin Luangwa ta Karonga.[3] Ya zama babban wurin jigilar bayi daga Afirka ta Tsakiya zuwa tafkin Malawi, sannan zuwa gabar tekun Swahili, inda suke ba da cinikin bayi a tekun Indiya da bayi. Mlozi ya ayyana kansa a matsayin Sarkin Musulmi na yankin da yake iko da shi.

Da farko Mlozi ya haɗa kai da mutanen Ngonde, amma daga baya suka shiga rikici. Ngonde ya kulla yarjejeniya da Birtaniya, waɗanda suka yi yunkurin samun tasiri a yankin a shekarun 1880.[4] Wannan ya haifar da yaki tsakanin Mlozi da Ngonde da kuma tsakanin Mlozi da Birtaniya.

A shekarar 1895 Turawan mulkin mallaka ne suka kashe Mlozi.[5]

  1. Stuart-Mogg, D., Shepperson, G. (2024). Mlozi of Central Africa: Trader, Slaver and Self-Styled Sultan.The End of the Slaver. Malawi: Luviri Press.
  2. Stuart-Mogg, D., Shepperson, G. (2024). Mlozi of Central Africa: Trader, Slaver and Self-Styled Sultan.The End of the Slaver. Malawi: Luviri Press.
  3. Stuart-Mogg, D., Shepperson, G. (2024). Mlozi of Central Africa: Trader, Slaver and Self-Styled Sultan.The End of the Slaver. Malawi: Luviri Press.
  4. Stuart-Mogg, D., Shepperson, G. (2024). Mlozi of Central Africa: Trader, Slaver and Self-Styled Sultan.The End of the Slaver. Malawi: Luviri Press.
  5. Stuart-Mogg, D., Shepperson, G. (2024). Mlozi of Central Africa: Trader, Slaver and Self-Styled Sultan.The End of the Slaver. Malawi: Luviri Press.