Jump to content

Mohammed Seddik Benyahia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Seddik Benyahia
Minister of Foreign Affairs of Algeria (en) Fassara

8 ga Maris, 1979 - 3 Mayu 1982
Abdelaziz Bouteflika - Ahmed Taleb Ibrahimi (en) Fassara
Finance minister of Algeria (en) Fassara

23 ga Afirilu, 1977 - 8 ga Maris, 1979
Abd al-Malek Tammam (en) Fassara - Muhammad Yala (en) Fassara
ambassador (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jijel (en) Fassara, 30 ga Janairu, 1932
ƙasa Aljeriya
Faransa
Mutuwa Turkiyya, 3 Mayu 1982
Karatu
Makaranta Jami'ar Algiers 1
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya, ɗan siyasa da nationalist (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa National Liberation Front (Algeria)

Mohammed Seddik Benyahia or Ben Yahia (Janairu 30, 1932 Mayu 3, 1982)[1][2][3] ɗan siyasan Aljeriya ne kuma ɗan gwagwarmayar kishin ƙasa a lokacin yaƙin Aljeriya. Bayan samun 'yancin kai ya zama Ministan Labarai (1967-1971), Ilimi mai zurfi (1971-1977), Kuɗi (1977-1979), da Harkokin Waje (1979–1982 ). [4]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 30 ga watan Janairu, 1932, a Jijel. [5] A lokacin yakin Aljeriya, ya taka rawar gani wajen fafutukar neman 'yancin kai na ƙasarsa. Ya kasance babban sakataren fadar shugaban ƙasa na gwamnatin wucin gadi ta jamhuriyar Aljeriya (GPRA) kuma memba na tawagar Aljeriya a shawarwari da gwamnatin Faransa a Evian a shekarar 1962. [6] Shi ne ke da alhakin jagorantar taron CNRA a Tripoli (Libya) a shekarar 1962. Bayan samun 'yancin kai na ƙasarsa, ya riƙe muƙamin jakadan Moscow da London. Ya jagoranci tawagar Algeria da suka kulla yarjejeniyar Algiers.

Ma'aikatun da ya riƙe

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Ministan Yaɗa Labarai daga shekarun 1967 zuwa 1971, Lokacin da ya shirya bikin Pan-African na farko a shekarar 1968.[7]
  • Ministan Ilimi da Bincike na Kimiyya daga shekarun 1971 zuwa 1977.
  • Ministan Kuɗi daga shekarun 1977 zuwa 1979. [7]
  • Ministan Harkokin Waje daga shekarun 1979 har zuwa rasuwarsa.[8]

A ranar 3 ga watan Mayun 1982, an harbo jirginsa a kan iyakar Iran da Turkiyya a lokacin da ya shiga tsakani a yakin Iran da Iraki.[9] Iran da Iraki dai sun musanta alhakinsu.[10]

  1. Jijel.info Archived 2007-10-17 at the Wayback Machine-Biographie de Mohamed Seddik BENYAHIA
  2. "Il y a 30 ans disparaissait Mohamed Seddik Benyahia". Le Matin d'Algérie. 4 May 2012.
  3. "Il y a 30 ans disparaissait Mohamed Seddik Benyahia". Le Matin d'Algérie. 4 May 2012.
  4. "hommage à Mohamed Seddik Benyahia : Fin politicien et diplomate de talent". El Moudjahid. 4 May 2016. Archived from the original on 23 January 2019. Retrieved 13 June 2017.
  5. "Mohamed Seddik Benyahia "le jeune renard"". El Djazair. 2017. Archived from the original on 2019-01-23. Retrieved 2017-06-13.
  6. "same reference above". Archived from the original on 2007-10-17. Retrieved 2008-08-14.
  7. 1 2 "Les argentiers de l'Algérie". Archived from the original on 2008-06-27.
  8. From University of Jijel Archived 2008-10-15 at the Wayback Machine (Arabic)
  9. "Mission Awry". Time Magazine. 1982-05-17. Archived from the original on October 25, 2012.
  10. "Il y a 30 ans, la mort tragique de Seddik Benyahia et de ses compagnons". Alterinfo. 25 May 2012. Archived from the original on 9 June 2025. Retrieved 9 June 2025.