Jump to content

Mohammed Sinwar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Sinwar
7. Izz ad-Din al-Qassam Brigades Chief of Staff (en) Fassara

16 Oktoba 2024 - 13 Mayu 2025
Mohammed Deif (mul) Fassara - ʻIzz al-Dīn al-Ḥaddād (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna محمد إبراهيم حسن السنوار
Haihuwa Khan Yunis Camp (en) Fassara, 16 Satumba 1975
ƙasa State of Palestine
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Gaza European Hospital (en) Fassara, 13 Mayu 2025
Yanayin mutuwa kisan kai (targeted killing (en) Fassara
hari ta jirgin sama)
Killed by Israeli Air Force (en) Fassara
Ƴan uwa
Ahali Yahya Sinwar (mul) Fassara da Zakariya Ibrahim Sinwar (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Shugaban soji da mujahid (en) Fassara
Mamba Izz ad-Din al-Qassam Brigades (en) Fassara
Aikin soja
Ya faɗaci 2006 Gaza cross-border raid (en) Fassara
Gaza war (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Hamas (mul) Fassara
IMDb nm17351530

Mohamed Sinwar (An haife shi a shekarar 1975) a binrinin Khan Younis. A lokacin yayansa Yhaya Sinwar na da shekara sha uku. Rikici ya sa iyayensu sun baro ƙauyensu da ke kusa da Ashkelon a shekarar 1948 inda suka koma da zama a kudancin birnin Gaza.

A shekarar 1991, an ɗaure Mohammed Sinwar a gidan yarin Isra'ila na Ketziot har tsawon wata tara saboda zargin sa da "ayukan ta'addaci".

A cewar jaridar the Jerusalem Post, Mohammed ya ƙara samun ƙwarin gwiwa da zimma tun daga lokacin da Hamas ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila a shekarar 2000 zuwa yanzu. Kamar dai ɗan'uwansa Yahya, shi ma Mohammed Sinwar ya yi suna a lokaci da shi Yahya ke zaman jarun a kurkukun Isra'ila.

Ya samu alaƙa da manyan kwamandojin Hamas da suka yi aiki a tare, cikin su har da Mohammed Deif, Saad al-Arabid, da wasu jagorori da suka bunƙasa ƙungiyar ta Hamas, in ji jaridar.

Jami'an gwamnatin Isra'ila sun ce Mohammed Sinwar na cikin waɗanda ake zargi da yin garkuwa da sojan nan Bayahude Gilad Shalit a 2006, abin da ya yi sanadiyyar aka saki ɗan'uwansa Yahya, bisa yarjejeniyar musayar fursunoni Falasɗinawa1,027.

Mohammed Sinwar ya shafe gomman shekaru yana faman ɓuya domin kaucewa sojojin Isra'ila daga kama shi ko kashe shi.