Jump to content

Muhammad Ahmad Mahgoub

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Muhammad Ahmad Mahgoub (Arabic: محمد أحمد المحجوب, romanized: Muḥammad Aḥmad al-Maḥjūb; 17 May 1908 – 23 June 1976[1]) Dan siyasar kasar wanda yaza Ministan harkokin wajan kasar da Kuma Prime Ministan Sudan na biyar. She sanannen marubuci ne, wanda ya wallafa rubutu masu yawa da yaran larabci.

An haife shi a garin Ed Dueim a shekarar 1908. Ya koma Khartoum yana da shekaru bakwai. Mahgoub ya kammala karatu daga makarantar injiniya a shekarar 1929 kuma a shekarar 1938, ya sami digiri na farko na Shari'a daga Kwalejin Gordon Memorial . An zabe shi a majalisa a shekarar 1946. Bayan samun 'yancin kai, Mahgoub ya kasance ministan harkokin waje tsakanin shekarar 1956 da 1958, sannan kuma tsakanin shekarar 1964 da 1965. A shekarar 1965, an zabe shi Firayim Minista, amma daga baya aka tilasta masa ya yi murabus. A shekara ta 1967, an zabe shi Firayim Minista a karo na biyu kuma ya yi aiki a wannan mukamar har zuwa juyin mulkin shekarar 1969.

Gwamnatin Mahgoub na 1965 tana da manufofi guda biyu: ci gaba ta hanyar warware Matsalar kudanci da kuma cire communists daga mukamai na iko. Sojojin sun kaddamar da babban hari don murkushe yan tawaye kuma a cikin tsari sun kara sunanta na zalunci tsakanin mutanen kudu. Mutane da yawa na kudanci sun ba da rahoton cin zarafin gwamnati a kan fararen hula, musamman a Juba da Wau. Sojojin Sudan sun kuma ƙone majami'u da gidaje, sun rufe makarantu, sun lalata amfanin gona kuma sun sace shanu.[2]

Manufofin yaki na Mahgoub a Sudan ta Kudu an nuna Yana dauke da matsanancin zalunci da kuma yin amfani da ta'addanci ba tare da nuna bambanci ba, ya kai matakin tashin hankalin da ba a taɓa fuskanta ba a kudu. Yaƙin neman zaɓen shi, wanda ya haɗa da kisan kiyashi a kan fararen hula na kudanci da fashi wanda ya lalata dukan garuruwa, wasu masana illimi sun bayyana shi a matsayin kisan kare dangi kuma an kwatanta su da hanyoyin Alphonse de Malzac, wani bautar White Nile na Turai na ƙarni na 19.

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Index Ma-Mam". www.rulers.org. Retrieved 2020-11-26.
  2. "About this Collection | Country Studies | Digital Collections | Library of Congress". Library of Congress, Washington, D.C. 20540 USA. Retrieved 2025-01-18.