Jump to content

Muhammad Bawa (Ɗan'ance)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Muhammad Bawa wanda aka fi sani da Ɗan'ance, (an haife shi a ranar 1 Junairun 1916, ya rasu a ranar 1 Junairun 1986) mawakin gargajiya ne na noma da dambe a Kasar Hausa daga arewacin Najeriya.[1][2]

Tarihin Waka

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ɗan'ance a kauyen 'Yan Tsakkuwa, garin Gandi da ke karamar hukumar Raɓa ta Jihar Sakkwato.[2] Ɗan'ance bai gaji kiɗi ba saboda mahifinshi ba makiɗi bane, ya gaji kiɗi ne daga wajen kanen mahaifiyarsa wanda ake kira da Anace, wanda shine ya riki Ɗan'ance tun daga yarintar sa. Kawun nasa wato Anace, wani shahararren makiɗin dambe ne wanda shine sarkin makaɗan 'Yar Tsakkuwa a lokacinshi

Bawa Ɗan'ance ya fara waka ne tun yana yaro matashi, kuma ya fara ne saboda tasowarsa a wurin kawun sa Anace kuma wakokin shi kuma sun fi karkata bangaren jarumta da bajinta na manyan 'yan wasan dambe irin su Dan Dunawa, Shago, da Ado dankore.[1] Da farko dai Ɗan'ance ya fara ne da kiɗin dambe, sannan daga baya ya watsar ya koma kiɗan noma. A kiɗin noma ne Bawa yayi fice duk da cewa daga baya ya koma kiɗan dambe inda ya hadu da su Muhammadu Shago da Ɗandunawa da sauran 'yan dambe da ya yi wa waka.[3]

  1. 1.0 1.1 "Dan Anace Profile and Discography | African Music Library". africanmusiclibrary.org. Retrieved 2025-08-26. https://africanmusiclibrary.org/artist/Dan%20Anace[permanent dead link]
  2. 2.0 2.1 "WAKOKIN NOMA NA BAWA DAN ANACE GANDI". Retrieved 2025-08-26. https://www.amsoshi.com/2023/08/waoin-noma-na-bawa-dan-anace-gandi.html
  3. Furniss, Graham (2022-02-15), "7. TIED SINGERS, SINGERS FOR COMBATANTS, FARMERS AND EMIRS", Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh University Press, pp. 166–191, https://www.degruyterbrill.com/document/doi/10.1515/9781474468299-012/pdf?licenseType=restricted&srsltid=AfmBOoqtfMucGK3dXbTkanMBxedxkEPtzeTMuclzGVyNT0orFxm4IZxv