Muhammad Garba
Muhammad Garba | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Kano, 25 Nuwamba, 1964 (60 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Muhammad Garba dan jarida ne kuma Dan Najeriya,[1] kuma dan siyasa daga jihar Kano wanda shine kwamishinan yada labarai.[2] kuma memba na Kwamitin Gudanarwa a Kungiyar Yan Jarida ta Duniya.[3]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Muhammad a ranar 22 ga watan Nuwambar shekara ta alif dari tara da sittin da hudu (1964) a Yakasai Quarters a Kano Municipal ta jihar Kano. Ya halarci Makarantar Firamare ta Kofar Nassarawa da Kwalejin Malamai, Sumaila ya yi Digiri na daya da na biyu a Jami'ar Bayero Kano.[4][5]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad ya fara aikin jarida a shekarar 1989 tare da Kamfanin Dillancin Labarai na Triumph, Kano a matsayin dan jarida kuma ya yi aiki a jihohi daban-daban na tarayya a matsayin wakilin. Daga baya ya girma a cikin aikinsa har ya zama Babban Edita, Editan Labaran Rukuni, da Mataimakin Edita.[4] Ya kuma taba zama memba na Hukumar Edita na Jaridun Kasa da dama. Muhammed Garba ya rike mukamai daban-daban da suka hada da Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a shekarar 1993 da Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 1999 zuwa 2003. Ya fara fafutukar sa na kungiyar ne a matsayin shugaban kungiyarsa ta Chapel-The Triumph, wacce ke karkashin kungiyar Yan jarida ta Najeriya (NUJ), jihar Kano. Daga baya aka zabe shi shugaban majalisar jiha na a wa’adi biyu kuma ya kasance mataimakin shugaban kungiyar na kasa, sannan ya zama shugaban kungiyar Yan jarida ta Najeriya NUJ a shekarar 2009. Muhammad ya kasance shugaban kungiyar Yan jarida ta yammacin Afirka (WAJA) wanda aka zaɓa a Bamako, Mali kuma shine shugaban kungiyar Yan siyasan jarida ta Afrika (FAJ) wanda aka zaba a Casablanca, Morocco 2009. Muhammad memba ne na Kwamitin Gudanarwa na Kungiyar Yan Jarida ta Duniya (IFJ) wanda aka zaba a Dublin, Ireland. Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada Muhammad kwamishinan yaɗa labarai a shekarar 2015.[6][7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://platinumpost.ng/2020/01/10/profile-muhammad-garba-the-kano-state-government-imagemaker/
- ↑ https://www.dailytrust.com.ng/kano-ganduje-retains-some-former-commissioners-in-new-cabinet.html
- ↑ https://thetriumphnews.com/meet-kanos-new-commissioners-i/[permanent dead link]
- ↑ 4.0 4.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-12-03. Retrieved 2021-05-20.
- ↑ https://platinumpost.ng/2020/03/02/the-journey-of-a-versatile-journalist-to-the-peak/
- ↑ https://www.kanostate.gov.ng/?q=portfolio/ministry-information-internal-affairs Archived 2021-05-20 at the Wayback Machine
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-15. Retrieved 2023-03-15.
- ↑ https://dailypost.ng/2019/11/05/ganduje-swears-in-new-commissioners/
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from March 2023
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Webarchive template wayback links
- Marubutan Najeriya
- Hausawa
- Gwamnonin Nijeriya
- Haifaffun 1964
- Rayayyun mutane
- Mutane daga jihar kano