Muhammed Dan Abba Shehu
Appearance
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Jihar Bauchi, 4 Disamba 1964 (61 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Hausa | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
Muhammed Dan Abba Shehu (an haife shi a ranar 4 ga watan Disamba 1964) ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai ta tarayya ta 10 mai wakiltar mazaɓar Zaki a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. [1]
A shekarar 2024, Shehu ya ɗauki nauyin kudirin neman magani kyauta ga mata masu juna biyu a cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a lokacin haihuwa da bayan haihuwa. Ya yi tsokaci kan rahoton Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), inda ya jaddada yawan mace-macen jarirai a Najeriya da kuma matukar buƙatar inganta tsarin kiwon lafiya, musamman ga mata masu juna biyu, "domin rage musu wahalhalu da kuma ƙara musu kwarin gwiwa". [2] [3] [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ YAKUB, ABDULRASHEED (2023-03-07). "INEC releases full list of elected lawmakers for Nigeria's 10th Assembly". Peoples Gazette Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-05-23.
- ↑ Twaki, Leah (2024-05-23). "Reps seek free healthcare for pregnant women". OrderPaper (in Turanci). Archived from the original on 2024-05-23. Retrieved 2024-05-23.
- ↑ "House Urges Health Ministry to Direct Free Medical Treatment for Pregnant Women – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2024-05-23.
- ↑ "Reps want free medical treatment for pregnant women - Daily Trust". Daily Trust (in Turanci). 2024-05-23. Retrieved 2024-05-23.