Jump to content

Muktar Muhammed

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muktar Muhammed
gwamnan, jihar Kaduna

1977 - ga Yuli, 1978
Usman Jibrin - Ibrahim Mahmud Alfa
Rayuwa
Haihuwa 11 Nuwamba, 1944
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 1 Oktoba 2017
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Muktar Muhammed (11 ga Nuwamban 1944 – 1 ga Oktoban 2017) [1] [2] ya kasance gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Nijeriya daga watan Yuli 1978 zuwa Oktoban 1979 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo. [3] Wing Commander Muktar Muhammed ya taka rawa sosai a juyin mulkin da ya kawo Janar Murtala Mohammed kan ƙaragar mulki, kuma an naɗa shi shugaban sabuwar Majalisar Koli ta Sojoji a ranar 30 ga watan Yulin shekarar 1975. [4] An kuma naɗa shi gwamnan jihar Kaduna a shekarar 1977, inda aka kara masa girma zuwa Group Captain. Ya yi ritaya daga aikin sojan saman Najeriya a matsayin Air Vice Marshal (AVM).[5]

  1. "AVM Mukhtar Muhammed dies at 73". www.dailytrust.com.ng. Archived from the original on 2017-10-03.
  2. https://www.pressreader.com/nigeria/daily-trust/20171003/281603830669660. Retrieved 18 December 2022 – via PressReader. Missing or empty |title= (help)
  3. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-05-20.
  4. Nowa Omoigui. "MURTALA RAMAT MUHAMMED (1938-1976)". Dawodu. Retrieved 2010-05-20.
  5. James O. Ojiako (1983). 1st four years of Nigeria executive presidency: success or failure. Daily Times of Nigeria. p. 225.

Hanyoyin haɗi na Waje

[gyara sashe | gyara masomin]