Jump to content

Munira al-Qubaysi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Munira al-Qubaysi
Rayuwa
HaihuwaDamascus, 1933
ƙasaSecond Syrian Republic (en) Fassara
United Arab Republic (en) Fassara
Siriya
MutuwaDamascus, 26 Disamba 2022
Karatu
MakarantaDamascus University (en) Fassara Digiri a kimiyya : biology
Damascus University (en) Fassara
HarsunaLarabci
Sana'a
Sana'aDa'awah (en) Fassara da malami
FafutukaMabiya Sunnah
Imani
AddiniMusulunci

Shaykha Munira Qubaysi (wacce akafi kira da suna Qubeysi; a harshen Larabci, ta rayu daga shekarar 1933 - 25 ga Disamba, 2022) . Malamar addinin Musulunci ce.

Qubaysi ta kammala karatun digiri na farko a fannin ilmin halittu da tsirrai a Jami'ar Dimashƙu a cikin shekarun 1950 a lokacin da matan da suke saka hijabi a makarantun jami'o'i ko dai ba su da yawa ko kuma ma babu su. Daga baya ta ƙara samun wani digiri a cikin fannin addinin Islama (shariah) kuma ta koyi kimiyyar Addinin Islama ta waje da ta ciki (Da'awar addinin Islama) daga wasu sanannun manyan malaman garin Dimashƙu.[1] An ba ta izini ko Sahalewa (ijaza) don koyarwa don koyarwa da tsarkake shiryarwa zuwa ga tsarkin zuciya . Ta kafa ƙungiyar da'awa me zaman kanta ta mata a lokacin da kuma take da haɗin gwiwa tare goyon bayan manyan shugabannin addinai na ƙasar Siriya a matsayin jagorar da'awar musulmi a cikin yankin ta. Bayan mutuwar ta da yawan manyan mazajen malaman addini a Siriya da wajen ta sun zo gaba don su yi ta'aziyya da kuma yabawa da aikin ta.[2]      

An haife ta ne a shekara ta 1938 daga mahaifinta dan Ƙasar Aljeriya, Muhammad ʿAlī Ḥusaynī al-Jazāʾirī, wanda masanin addini ne kuma masanin Fiƙihu. Ta sami digirin ƙwarewa (PhD)a fannin lissafi daga Tarayyar Soviet . Ta koma gida ta koyar na ɗan ƙaramin lokaci a Aljeriya kafin ta auri wani mutumin Siriya kuma takoma da zama garin Damascus inda a can aka nada ta a matsayin farfesa a fannin lissafi a Jami'ar Damascus . [3]

  1. ↑ Institute, Rabata (29 December 2022). "Shaykha Munira bint Hamdi Qubaisi [1933-2022]: Pioneering Mujaddida, Learned Scholar, And Beloved Mentor – An Obituary". MuslimMatters.org (in Turanci). Retrieved 2 January 2023.
  2. ↑ Institute, Rabata (29 December 2022). "Shaykha Munira bint Hamdi Qubaisi [1933-2022]: Pioneering Mujaddida, Learned Scholar, And Beloved Mentor – An Obituary". MuslimMatters.org (in Turanci). Retrieved 2 January 2023.
  3. ↑ "Al-Hafiza Al-Jami'a Dr Da'ad Al-Husayni (1938-2009)". On the Path of Knowledge (in Turanci). 2013-03-31. Retrieved 2023-01-05.