Muri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muri


Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaTaraba state
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Muri, gari ne wanda yake da masarautar gargajiya a Jalingo kuma tana da sarautar lamba ɗaya wato (Emir) garin ya mamaye karamar hukumar Karim Lamido ARDO KOLA Yoro, karamar hukumar Taraba da sauran su, garin yana arewa maso yammacin jihar Taraba a gabashin Najeriya, kimanin tsakanin 9° da 11° 40′ E. da 7° 10′ da 9° 40′ N.Kogin Benuwai na kusa da garin miuri yankin kudancin kogin shi yake shayar da kogunan da suka fito daga yankin Kamaru zuwa Binuwai. A cikin shekara ta 1991, an kuma kiyasta garin yana da yawan jama'a 56,570. Sai dai kwarin Benuwai yana da yanayin da turawa basa iya zama ba a garin, sai dai kuma akwai wurare a arewacin lardin, kamar ƙauyen Fula na Wase a kudancin tsaunukan Murchison, wanda wannan kuma wurin yana bada yanayi mai kyau.[1][2] An fi amfani da harsunan Tula–Waja irin su Dadiya da Bangwinji ana magana da su gefen tsaunukan Muri.

Tarihin Muri[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 1817, aka kafa garin Muri a matsayin wanda Fulani ne suka kafa shi bayan jihadinsu.[3] Daga shekarar 1892 zuwa 1893 ƙasar Faransa tazo garin da sunan kariyar ta gaskiya, ƙarƙashin Gwamna Louis Mizon (b. 1853 - d. 1899). A cikin shekara ta 1901 garin yanda faɗi kusan 25,800 m². lardin da ke ƙarƙashin mulkin Birtaniya na Arewacin Najeriya, mai iyaka daga kudu (a) sai daga Kudancin Najeriya, kudu maso gabas (SE) sai ta gabas (E) tayi iyaka da yankin Kamaru wanda Jamus ta mulka. Sai Arewa (N) ta lardin Yola.[1] Sai ta yamma (W) tayi iyaka da Bauchi. Sai yamma kuma tayi iyaka da wani yankin Nasarawa da Bassa mai kimanin mutane 828,000. Ƙaramar masarautar Katsena-Allah ta kai kudu da Benuwai sosai yamma da 9° E., gwargwadon iyakar sauran lardin. Lardin yana da arzikin dazuzzuka, kuma Kamfanin Neja yana kula da tashoshin kasuwanci a gaɓar kogin. Ana noman auduga, saƙa da rini sauran su wannan yaba mutane damar samun aiki ga dubban mutane. Haka Lardin Muri ya haɗa da tsohuwar daular Jukun tare da ƙananan garuruwan Fulani daban-daban da kuma wasu ƙabilun maguzawa, waɗanda a cikinsu akwai ‘yan ƙabilar Munshi waɗanda suka mamaye lardunan Nassarawa da Bassa, na cikin waɗanda suka fi fama da tashin hankali. Yan ƙabilar Munshi sun mamaye kusan m² 4000, a gundumar Katsena-Alah. Ƙabilun maguzawa a arewacin lardin sun kasance suna cin naman mutane, marasa bin doka da oda, waɗanda suka daɗe suna nuna fushinsu da kashe-kashenn ’yan kasuwa masu fatauci zuwa Bauchi suna cikin haɗari, kuma sun daƙushe kasuwannin kwarin Binuwai (Benue valley) da Kamaru daga jihohin Hausa duk Hanyoyin da suka san ana bi sai da suka tare ta, daman hanyoyi biyu ne kawai, ɗaya ta Wase ɗayan kuma ta Gatari. A kudancin lardin maguzawa makiya sun rufe hanyar shiga Kamaru sai ta hanyoyi biyu, Takum da Beli. Ƴan kasuwan Hausawa na lardin Muri yana masu wahala bin wannan waɗannan hanyoyin ga haɗari da kashe-kashe an sami sauƙi sune a lokacin da gwamnatin Birtaniya tazo.

Muri ya zo ne a ƙarƙashin mulkin Birtaniya a shekara ta 1900. Babban yunƙurin gwamnatin shi ne taimakawa wajen buɗe hanyoyin kasuwanci. A cikin shekara ta 1904 wani balaguro da aka yi kan masu cin naman mutane ya haifar da kame manyan sansanoninsu da matsugunai tare da buɗe kasuwannin manyan gundumomi, hanyoyin da ke zuwa Binuwai sun kasance babu matsala lami lafiya. A cikin shekara ta 1905 wani balaguron yaƙi da Munshi, wanda ya zama dole ta hanyar kai hari ba gaira ba dalili a tashar Kamfanin Neja a garin Abinsi. Rashin wata hukuma ta tsakiya ya jinkirta aiwatar da shirin mayar da lardin ƙarƙashin kulawar masu gudanarwa. An kuma tsara gwamnatin a bisa tsari irin na sauran Arewacin Najeriya, kuma a ƙarƙashin wani Bature. An raba shi zuwa sassa uku na gudanarwa - gabas, tsakiya da yamma - tare da hedkwatarsu a garin Lau, Amar da Ibi. An kafa kotunan shari'a na lardi da na asali. An kai telegraph din zuwa garin Muri. Muri na ɗaya daga cikin lardunan da cinikin bayi ya fi ƙarfi a cikinsu, kuma matsayin da yake tsakanin ƙasar Jamus da ƙasashen Hausa ya sanya ta a farkon gwamnatin Burtaniya ta zama hanyar da aka fi so wajen safarar bayi.[1]

Sarakunan Muri[gyara sashe | gyara masomin]

Sarakunan Muri
No. Sunan mai mulki Fara mulki Ƙarshen mulki
1 Hamman Ruwa dan Usman 1817 1833
2 Ibrahim dan Hamman Ruwa 1833 1848
3 Hamman dan Hamman Ruwa 1848 1861
4 Hamadu dan Bose 1861 1869
5 Burba dan Hamman 1869 1873
6 Abubakar dan Hamman Ruwa 1873 1874
7 Muhammadu Nya dan Abubakar 1874 1897
8 Hasan dan Muhammadu Nya 1897 1903
9 Muhammadu Mafinɗi dan Muhammadu Nya(Honorary Knight Commander of the Order of the British Empire, Awarded by King George V ) (b. 1868 – d. *1953)[4] 1903 1953
10 Muhammadu Tukur dan Muhammadu Nya 1953 25 Oktoban 1965
11 Umaru Abba Tukur 6 Nuwamban 1965 12 Augustan 1986 (sauke shi akayi)
12 Alhaji Abbas Njidda Tafida 13 Yuni 1988 har zuwa yanzu

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2  One or more of the preceding sentences incorporates text from a publication now in the public domainChisholm, Hugh, ed. (1911). "Muri". Encyclopædia Britannica. 19 (11th ed.). Cambridge University Press. p. 35.
  2. Kleinewillinghöfer, Ulrich. 2014. The languages of the Tula – Waja Group. Adamawa Languages Project.
  3. Victor N. Low (1972). Three Nigerian Emirates: A Study in Oral History. Northwestern University Press. p. 100. ISBN 978-0-810-1037-19.
  4. "Mafindi website". Archived from the original on 2020-11-25. Retrieved 2022-02-12.

Mahaɗar link ta waje[gyara sashe | gyara masomin]

WorldStatesmen - Nigeria

Template:Nigerian traditional states