Musa Mohammad
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa |
Bagan Datuk (en) |
| ƙasa | Maleziya |
| Mutuwa |
Petaling Jaya (en) |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
| Imani | |
| Jam'iyar siyasa |
United Malays National Organisation (en) |
Tan Sri Dato 'Seri (Dr.) Musa bin Mohamad [1] ( Jawi : موسى بن محمد) ya kasance ɗaya daga cikin membobin Majalisar Koli ta UMNO a tsakanin 2000 da 2003. Ya kuma kasance tsohon Ministan Ilimi kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kwalejin, Universiti Sains Malaysia .
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Ya sami Digiri na farko a kan ilimin hada magunguna (wato pharmacy) a Jami’ar Singapore [2] a 1962 da kuma Master of Science Degree a Pharmaceutical Technology daga Jami’ar London a shekarar 1972.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Musa Mohammad ya kware a fannin koyarwa da gudanarwa na tsawon shekaalru 20 a Universiti Sains Malaysia. Har wayau ya rike matsain Dean na Pharmacy na Universiti Sains Malaysia (USM) daga shekarar 1975 to 1979. Ya kuma riqe matsayin Deputy Vice Chancellor (Academic) kafin a bashi Vice Chancellor from 1982 to 1998.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Firayim Ministan Malaysia, Tun Dr. Mahathir Mohamad ne ya nada shi matsayin Sanata a shekarar 1999. Sannan, an nada shi matsayin Ministan Ilimi daga 1999 zuwa 2003. Tun Abdullah Ahmad Badawi ya tsawaita mukaminsa na minista har zuwa 2004.
Bayan ritaya
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati, an nada shi a matsayin Shugaban wasu kamfanoni kamar Polyglass, Universiti Telekom Sdn Bhd (shi ma darekta). Ya kuma kasance Shugaban Kamfanin Mai Zaman Kansu & na Shugabancin Pelikan International Corporation Berhad daga 2005 zuwa 2012.
Lambobin yabo
[gyara sashe | gyara masomin]Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jami'ar (KUSTEM), Jami'ar Malaysia Sabah (UMS), Kwalejin Kwalejin Injiniya ta Arewacin Malaysia (KUKUM) ta ba shi digirin girmamawa na 7 a fannin kimiyya; a cikin ilimin fasaha ta Jami'ar Multimedia (MMU); a cikin falsafar ta Kwalejin Jami'ar Tun Hussein Onn (KUITTHO); da ilimi ta Jami'ar UCSI. Tan Sri Musa shi ma ya kasance ɗan’uwan ƙungiyar likitancin Malaysia ne da Kwalejin Kimiyya. [3]
Daraja na Malaysia
[gyara sashe | gyara masomin]
Malaysia : Commander of the Order of Loyalty to the Crown of Malaysia (P.S.M.) (1994)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ Bloomberg profile
- ↑ NUS alumni profile
- ↑ "Member: Tan Sri Dato' Seri (Dr.) Musa Mohamad". Archived from the original on 2020-02-01. Retrieved 2021-06-06.