Musa N'Daw

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Moussa N'Daw (an haifeshi ranar 15 ga watan Yuli, 1968) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba. Ya yi aikinsa a gasar lig ta Morocco, a Wydad Casablanca a tsakanin shekarar 1991 zuwa 1992 da kuma a cikin ƙwararrun Saudiyya a tsakanin 1992 zuwa 1994 tare da Al-Hilal da 1999 zuwa 2000 tare da Al-Ittifaq. Yanzu shi koci ne a Senegal tare da Jeanne d'Arc a Dakar.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]