Mustapha Stambouli
![]() | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 10 ga Maris, 1920 | ||
ƙasa | Aljeriya | ||
Mutuwa | 20 ga Afirilu, 1984 | ||
Sana'a | |||
Sana'a |
ɗan siyasa da nationalist (en) ![]() | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | National Liberation Front (Algeria) |
Mustapha Stambouli (10 ga Maris, 1920 a Mascara, Aljeriya - 20 ga watan Afrilu, 1984 a Mascara, Aljeriya) jagoran kishin ƙasa ne na Aljeriya.[1][2][3]
Ɗalibin shari'a, ya kasance mai fafutukar neman kishin ƙasa daga karshen shekarar 1930s a cikin Parti du peuple algérien (PPA), kuma hukumomin 'yan mulkin mallaka na Faransa sun ɗaure shi sau da yawa. A cikin shekarar 1948, an kama shi a kan iyakar Libya, yayin da yake kokarin shiga cikin 'yan tawayen Larabawa a Falasdinu. Ya shiga cikin Front de Liberation nationale (FLN), kuma ya yi aiki a matsayin jami'i a reshenta na makamai, Armée de Liberation nationale (ALN), a lokacin Yaƙin 'Yancin Aljeriya (1954-62).[4][5][6] Daga ƙarshe ya zama sakataren gwamnati a cikin Gouvernement provisoire de la republique algérienne (GPRA), gwamnatin gudun hijira da FLN ta kafa. Bayan samun 'yancin kai a shekarar 1962, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai, amma bai taka rawar siyasa ba bayan haka.
Yanzu haka akwai wata jami'a mai sunansa a garinsu na Mascara a ƙasar Aljeriya.[7][8][9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Quandt, William B. (1968). The Algerian Political Elite: 1954-1967 (in Turanci). p. 206. Retrieved 30 October 2024.
- ↑ Bedjaoui, Mohammed (1961). Law and the Algerian Revolution (in Turanci). International Association of Democratic Lawyers. p. 74. Retrieved 30 October 2024.
- ↑ Jackson, Henry F. (12 May 1977). The FLN in Algeria: Party Development in a Revolutionary Society (in Turanci). Bloomsbury Academic. p. 50. ISBN 978-0-8371-9401-1. Retrieved 30 October 2024.
- ↑ Quandt, William B. (1968). The Algerian Political Elite: 1954-1967 (in Turanci). p. 206. Retrieved 30 October 2024.