Mutanen Yanzi
![]() | |
Yankuna masu yawan jama'a | |
---|---|
Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Ƙabilar Bayanzi (ko Yan, Yanzi, Yansi) ƙabila ce a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo waɗanda ke zaune a kudu maso yammacin ƙasar kuma sun kai kusan miliyan bakwai.
Yanzi suna magana da Kiyansi (ko Eyans), harshe a cikin dangin Bantu. Bangaren siyasa mafi girma shine sarauta, wanda akwai kimanin 120 a karkashin sarakunan gargajiya 3 wanda mafi shahara daga cikinsu shine sarki Kinkie ko Binkie wanda sabon jigon sa shine Mfum' ngol' ko Mfumu ngolo kamar yadda Turawa suka furta (wanda aka fassara da "babba ko sarki mai ƙarfi") daga yankin Kidzweme, kuma kwanan nan magajinsa Mfum' Ntwàl Moka Ngol' Mpat', masanin tattalin arziki wanda aka horar a Harvard.
Bayanzi suna gudanar da tsarin yara zasu kasance 'yan ahalin uwa, don haka yaro yana cikin dangin uwa.
Matafiya 'yan mulkin mallaka na Belgium sun fara cin karo da su ne a Bolobo da ke kogin Kongo, a matsayin 'yan kasuwa a sama da kasan kogin. Sun dauke su aiki daga 1883, da farko a matsayin masu gadi. Bayan haka, an tilasta wa Bayanzi yin aikin noman shukar kwakwar manja, daga baya kuma aka yi amfani da su a matsayin magatakarda ko masu fassara.
Kabilanci
[gyara sashe | gyara masomin]'Yan kabilar Bayanzi al'ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ne a kudu maso yammacin kasar, wadanda ke magana da yaren Bantu.[1]Sauran sunayen su sun hada da Batende, Bayansi, Mbiem, Nkaan, Wachanzi, Yansi, Yanzi, Yey.[2]
Yanki
[gyara sashe | gyara masomin]‘Yan Jesuit sun rubuta al’adun gida na Bayansi, wanda da alama sun nuna cewa sun samo asali ne daga gaurayawan yankin Arewa (Sudan ta yanzu) ko Arewa maso Yamma (Gabon ta yanzu) ta hanyar hada auren sarakunan kabilu, a yankin da suka kira “Kimput” wanda ke nufin "Europa" kuma da alama yana nufin Masar (Hut-Ka-Ptah) ko Habasha "Punt". Sun yi magana game da wani babban kogi wanda ruwansa mai gishiri ne wanda har manyan kwalekwalen jiragen ruwa ba su iya hayewa. Wataƙila wannan yana nufin Tekun Atlantika ko kogin Nilu ko ma duka biyun. Sun ce sun yi zaman bauta a ƙasar Kong Mukoko, sannan suka zama yan kasuwa a bakin tafkin Malebo.[3]