Jump to content

Mutiu Shadimu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mutiu Shadimu
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

ga Afirilu, 2015 -
District: Oshodi/Isolo I
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Mutiu Shadimu ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Oshodi-Isolo I bayan ya zama zakara a zaɓen Najeriya na shekarar 2015 a watan Afrilu a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar People's Democratic Party. [1]

Mutiu ya halarci kwalejin Egba da ke Ilaro a jihar Ogun inda ya samu shaidar kammala karatunsa na babbar makarantar Afirka ta Yamma a shekarar 1985. Shi ma'aikaci ne a Cibiyar Kula da Haraji ta Najeriya da Cibiyar Haraji ta Najeriya.

Aiki da siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin ya zama ɗan Majalisar Wakilai, ya kasance mai ba da shawara na Auditor, Tax and Management. A zaɓen shekarar 2015, ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP kuma ya lashe zaɓen mazaɓar tarayya ta Oshodi-Isolo I. [2]

  1. Nigeria, Media (2018-06-06). "Biography Of Mutiu Shadimu". Media Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-07-09.
  2. Ezeamalu, Ben (2019-02-25). "Agbaje berates INEC over late release of Lagos election results" (in Turanci). Retrieved 2020-07-09.