Gobalakrishnan Nagapan (an haife shi a ranar 23 ga watan Maris na shekara ta 1960), wanda kuma aka fi sani da N. Gobalak Krishnan, ɗan siyasanMalaysia ne.[1] Ya kasance memba na majalisar dokokin Malaysia na mazabar Padang Serai a Kedah daga 2008 zuwa 2013. An zabe shi a majalisar dokoki a matsayin memba na Jam'iyyar Adalci ta Jama'a (PKR) a cikin hadin gwiwar adawa ta Pakatan Rakyat, amma a shekarar 2011 ya bar jam'iyyar ya zauna a matsayin mai zaman kansa. Gobalakrishnan a ranar 8 ga Mayun shekarar 2017 ya koma Majalisa ta Indiya ta Malaysia (MIC) bayan ya bar ta shekaru 18 da suka gabata don shiga PKR.