Nafisat Abdullahi
Nafisat Abdullahi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jos, 23 ga Janairu, 1991 (33 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | Jahar Kaduna |
Karatu | |
Makaranta | London School of Photography (en) |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Nafisat Abdullahi,[1] Asalin sunanta shi ne Nafisat Abdurrahman, Abdullahi Amma an fi saninta da Nafisat Abdullahi ko Kuma Nafisa Sai Wata Rana.[2][3][4] An haife ta a ranar 23 ga watan janairu a shekara ta alif Ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991.
Jaruma Nafisa ta fito a fina -finai da Dama irin su
Sai wata Rana
Madubin dubawa[5]
Burin Raina
Shiri mai Dogon zango Labarina
Ƴa Daga Allah,
Haihuwa.
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi jaruma Nafisat abdullahi a ranar 23 ga watan Janairu a shekara ta dubu ɗaya da ɗari Tara da casa'in da buyu 1992. Ta kuma fara karatun ta na secondary a garin Jos Kuma ta karasa a Abuja. A shekarar 2013 an dakatar da ita daga shirin fina finan kannywood saboda ta karya doka.[6][7]
Ilimi.
[gyara sashe | gyara masomin]Ta karanci theater art a jami,ar Jos, sannan ta karanci ilimin ɗaukan hoto a landan a makarantan ɗaukan hoto dake Birtaniya.
Fim.
[gyara sashe | gyara masomin]Nafisat abdullahi ta fara harkar film ne tun lokacin tana yar shekara sha takwas Kuma film ɗin da ya fito da ita shine SAI WATA RANA a shekara ta 2010 a ƙarƙashin kamfanin FKD PRODUCTION Wanda Ali Nuhu ya bada umarni. Ta bayyana a cikin wani najaerian film wato Nollywood Mai suna Blood and Heyna Wanda Kenneth Gyang ya bada umarni, tare da Ali Nuhu da Kuma Sadiq Sani Sadiq.
Ta fito a cikin fim ɗin da Aminu saira ya bada umarni wato ‘Ya daga Allah’ da kuma ‘Kalamu wahid’ a shekarar 2014.[8][9]
Fina finai.
[gyara sashe | gyara masomin]- abarina Series [10]
- Sai Wata Rana
- Toron Giwa
- Ummi
- Zango
- Ya daga Allah
- Yar Agadez
- Addini ko Al'Ada
- Ahlul Kitab
- Alkawarina
- Alhaki Kwiukwiyo
- Alhini
- Allo (film)
- Auren Tagwaye
- Baban Sadik
- Badi Ba Rai
- Ban Kasheta Ba
- Blood and Henna
- Cikin Waye?
- Dan Almajiri
- Dan Marayan Zaki
- Dare
- Dawo Dawo
- Farar Saka
- Fataken Dare
- Gabar Cikin Gida
- Haaja
- Har Abada
- Jari Hujja
- Laifin Dadi
- Lamiraj
- Madubin Dubawa
- Guguwar So
- Baiwar Allah.
- Maimunatu
Lamban girma.
[gyara sashe | gyara masomin]Ta samu kyaututtukan girmamawa da dama irin su City People Entertainment Award 2013, sannan ta kasance jaruma ta ɗaya a masana'antar Kannywood a shekara ta dubu biyu da sha huɗu 2014. Jarumar ta karɓi kyautar girmamawa ta AMMA award a shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, MTN award a shekara ta dubu biyu da sha shida 2016, da Kuma Afro Hollywood award a shekara ta dubu biyu da sha bakwai 2017. Nafisa Abdullahi tayi soyyaya da Adam Zango har tayi burin aurenshi [11]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://x.com/NafisatOfficial?ref_src=twsrc%5Egoogle%7Ctwcamp%5Eserp%7Ctwgr%5Eauthor
- ↑ Team, 360hausa (2021-11-07). "BREAKING: Nafisat Abdullahi Launched "Nafcosmetics" As Her New Official Business". 360hausa.Com (in Turanci). Retrieved 2022-03-15.
- ↑ fynanse, fynanse (2023-08-24). "Nafeesat Abdullahi Biography And Net Worth". Nanablog.com.ng (in Turanci). Archived from the original on 2023-08-25. Retrieved 2023-08-25.
- ↑ "Nafisa Abdullahi Biography | Age | Net worth | Parent | Naijabiography". Naijabiography Media (in Turanci). Retrieved 2022-07-24.
- ↑ https://hausa.legit.ng/news/1467161-baki-da-ilimin-addini-fati-slow-ta-shigarwa-sarkin-waka-ta-yiwa-nafisa-abdullahi-wankin-babban-bargo/
- ↑ "Ku daina haihuwar 'ya'yan da ba za ku iya kula da su ba - Nafisa Abdullahi". BBC News Hausa. Retrieved 2022-08-04.
- ↑ http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/139399-kannywood-producers-suspend-star-actress-nafisa-abdullahi-for-organising-party.html
- ↑ http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/142503-kannywood-producers-lift-suspension-on-nafisa-abdullahi.html
- ↑ http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/hausa-movies-arts-entertainment/185172-nafisa-abdullahi-confirms-romance-with-adam-zango.html
- ↑ "Wakokin Labarina Series". Archived from the original on 2022-02-12. Retrieved 2022-02-12.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/news/2015/06/150616_nafisah_abdullahi_kannywood